Jamila Da Jamilu A cikin aji, a makarantar yara ta elementare, - TopicsExpress



          

Jamila Da Jamilu A cikin aji, a makarantar yara ta elementare, bayan malama ta gama koyarwa sai take tambayar dalibai; Malama: Jamilu me kake so ka zama idan ka gama karatu ka girma? Jamilu: Ina som nayi kudi kamar Dangote, na gina katon gida, na sayi jirgi da motoci, matata kuwa duk sati sai taje kasashen waje kamar su Paris, London, Spain, Dubai, Abu Dhabi, Madrid, Saudiyya, na …… (bai gama bayani ba malama ta katse shi) Malama: Yi mana shiru da shegen son kudi.. (sai malama ta juya wurin Jamila) Jamila idan kin girma mai ki ke so ki zama? Jamila: (cikin sanyin murya) ina so na zama matar Jamilu. Malama ta rike baki cikin mamaki da tunani, ta ce a ranta, ah! Duniya ta lalace, son kudi da son jin dadin duniya yanzu babu banbanci tsakanin manya da yara. To yanzu idan Jamilu ya zama shugaban al’umma nan gaba, me kuke sa ran zai faru? To ina mafita? ALLAH YA KYAUTA. (NAJBOY) @2go najboykhan
Posted on: Wed, 18 Sep 2013 08:40:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015