KALAMAN SHEIKH MARIGAYI JAAFAR YANA I GOBE.... Wajibi ne akan - TopicsExpress



          

KALAMAN SHEIKH MARIGAYI JAAFAR YANA I GOBE.... Wajibi ne akan shugaba ya tsare wa wadanda ya ke mulka rayuwar su, ta yadda za su iya barci har da mun shari a gidajen su. Saboda samar da tsari na tsaro mai inganci, ta hanyar kare hannun duk wadanda aka san kai-ka-won su, zai iya zama barazana ga al’umma. Ta hanyar tabbatar da doka ga dukkan wanda ya ke yiwa dokar karan tsaye. Duk wanda ya firgitar da wani ko wasu ya hana su yin barci a kowane dalili, ko ta hanyar karbar dukiyar sa, ko a dalilin murdiya da jayayya, ko a dalilin kabilanci, ko wani dalili na daban. To ya kasance shugaba ya hukunta, wannan wanda ya hana wasu barci.” Ko kadan marigayi Ja’afar Mahmud Adam, ba shi da masaniya a lokacin da yake furta wadannan lafuzza cewar, ‘yan sa’a’o’I kadan ne suka rage masa ya amsa kiran mahaliccin sa. Domin ya fade su ne a daren alhamis 12/04/2007 a yayin gabatar da taron wa’azi na musamman, da majalisar Ahlus-Sunnah ta shirya, domin yin bayanai akan ragowar babban zabe na musamman. Kasancewar dawowar sa kenan daga jihar Bauchi, ya zo wajen a makare, don haka ya takaita batun sa, ko don cewa da ya yi duk yawanci abinda zai fada, ‘yan’uwansa sun fada. Kamar yadda ake yi masa a duk lokacin da ya halarci kowane majalisi, gabatar da sunan sa ke da wuya, gaba daya wajen ya dau kabbarori. Kuma a cikin jawaban sa, ya tabo muhimman batutuwa da suka shafi hakkin shugaba akan talakawan sa, da kuma suma hakkin shugaba akan su. Kasancewar dama an shirya wa’azin ne bayan sallar Magariba zuwa Isha’I, ana kammalawa, aka umarce shi da ya jagoranci sallah. #abu_hafsat
Posted on: Fri, 29 Nov 2013 08:40:14 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015