KANA SON KA SACE ZUCIYAR MACE..? part (1). To Saurara kaji - TopicsExpress



          

KANA SON KA SACE ZUCIYAR MACE..? part (1). To Saurara kaji Jirgi na Masoya a‘a janye kanka mana, ai ba rada zan yi ma ba. Fada zan har na gefe ma su ji. | | | | | | | | | E, kwarai kuwa, ai an ce in ana yi wa mai uwa fada maraya ma sai ya kasa kunne ya ji. | | | | | | | | | Na san ka dade kana son aure, yara ‘kannenka duk sun yi aure har sun haihu, kana nan jiya ya yau! Duk farkon watan Ramadana sai ka yi kwarya-kwaryar balaguro, sobada kar yara su kada ma gwauro! | | | | | | | | | Allah sarki A‘a ture maganar bakin jini, kowa jininsa ja ne. | | | | | | | | | Ha ha ha uban wa ne zai ma wani asiri. | | | | | | | | | Yauwa to tsaya ma, da asirin yana yi sau nawa ka sa almajirai suka bude munjaye da hakuri suka rubuta sunan Tasalla a ciki? | | | | | | | | | Ta ta6a yi ma kallon so ko sau daya? | | | | | | | | | A‘a ai ba maganar wulakanci ba ne, | | | | | | | | | e, yauwa to saurare ni da kunnen basira. | | | | | | | | | Ka ta6a zuwa kamun kifi a kogi? | | | | | | | | | Madalla to wannan fatsar ko ‘kugiya da ake jefawa cikin ruwa, haka kawai ake jefa ta? | | | | | | | | | Yauwa dan gari, to wannan naman(tana) da ake makalawa a jiki ai shi yake janyo hankalin kifi. | | | | | | | | | Ko ba ka fahimta ba? Uhm! Ai abin sai da dabara. | | | | | | | | | Ka san me ya sa namijin tattabara yake wake matarsa? | | | | | | | | | Ko ka san me ya sa Talotalo yake tayar da tozonsa? | | | | | | | | | Ka ta6a lura da dalilin da ya sa ‘Dawisu yake baza gashin jelarsa? | | | | | | | | | Ba ka san me ya sa Zakara yake cin tsakuwa ya ba wa kaza ‘kwaya ba? | | | | | | | | | Uhm, to an bar ka a baya! Amma kai daga jin yadda na dauki hanyar nan ka tabbata zan sauke ka a tashar da za ka samu mata cikin sauki. | | | | | | | | | In dai mace ce to sai ma ka za6a ai. | | | | | | | | | Kwantar da hankalinka! hikima ce kawai za tai aiki, ba guru ba laya. | | | | | | | | | Ai daga yau ka daina wahalar diban ‘kasar da ta taka da tafin ‘kafarta. Ka bar wasu ‘yan tofe-tofe da kake a jikin cingam ka aika mata. | | | | | | | | | Ka daina wahalar barbada garin magani a jikin nama ka aika gidansu. | | | | | | | | | Ha ha ha, ai ba ma ci take yi ba! Ka ga, ciro wannan tsumman da ka sa a aljihu, da kake burga da shi da sunan kudi. | | | | | | | | | E, ai na gane ka ba tun yau ba. Amma wannan ba dabara ba ce, ai idan an ga kudi a aljihunka kuma ba ka bayarwa ka zama matsolo ke nan. Ka ta6a ganin aljihu a jikin zakara? To me yasa kaza take bin sa kullun? To yanzu kuwa za ka sani.. Hambal uba BBM pin 7A834FEE
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 21:22:22 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015