KIRA GA DUK WANI MUSULMI DA YA YARDA DA ALLAH DA GASKIYAR ANNABTAR - TopicsExpress



          

KIRA GA DUK WANI MUSULMI DA YA YARDA DA ALLAH DA GASKIYAR ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD S.A.A.W. ***************************** ***************************** Ya kai dan Uwa Musulmi mai albarka, wanda ya yarda, ya gaskata addinin Musulunci, ya amince da gaskiyar Manzancin Fiyayyen halittu, cikamakin Annabawa, Annabin Allah Muhammad mai tsira da aminci, ina amfani dawannan dama domin jawo hankalinka da nusar dakai wani Muhimmin al,amari danganeda abinda ya shafi MUMMUNAR AKIDAR NAN TA SHI,AH! Hakika ko shakka babu duk wani cikakken Musulmi mai hankali, mai Ilimi, mai Ilimi, wanda yasan darajar addininsa na Musulunci, yasan girman Allah da Manzonsa s.a.a.w yasancewa AKIDAR SHI,AH BA AKIDAR MUSULUNCI BACE! Shi,ah wata Mummunar Akida ce da MAKIYA ALLAH, MAKIYA MUSULUNCI suka assasata domin rushe ginin Musulunci. Ya dan uwa Musulmi hakika ya isheka Misali irin yadda Yan Shi,ah suka tsananta adawa suka tsananta gaba ga Sahabban Ma,aiki s.a.w, suka karyata ayoyin Alkur,ani da hadisan Manzon Allah s.a.w Ingantattu da sukai bayani akan Falala da Darajar Sahabbai, sukayi musu hukunci da wutar jahannama bayan Allah yayi musu hukunci da Aljannah, Yan Shi,ah suka Keta haddin Matan Manzo s.a.w, suka kaga musu abinda Allah ya kore musu, suka wulakantasu bayan Allah ya girmamasu, haka nan ya isheka misali irin yadda yan shi,ah suka maida munanan abubuwa da Musulunci yayi hani, ya tsoratar amatsayin haramun suka maidasu addini, danuwa hakika irin munanan akidun Shi,ah suna da yawa, kullum Malamai sunata tunatarda bayin Allah akansu guji, su nisanci wannan Muguwar akida ta Shi,ah. Hakika muni da gubarda ke cikin Mummunar akidar Shi,ah sai wanda yake karanta littafansu, yake sauraron Malamansu. Abinda nakeson kaiwa agareshi shine: duk Musulmin kirki, mai son Allah da Manzo s.a.w mai kishin Musulunci dole, wajibi, tilas yayi TAWAYE, ya nuna rashin goyon bayansa, ya nuna kiyayyarsa da adawarsa afili ga Mummunar akidar Shi,ah, ya nuna kiyayya da adawa ga Ma,abotanta wato Yan Shi,ah koda makusantansane. Shin yanzu ya dan uwa musulmi zaka yarda da Musuluncin wanda yake ganin rashin cikarAlkur,ani??? Wanda yake kafirta Sahabbanda suka kasance tareda Annabin Allah, suka taimakeshi, Annabi ya amince dasu, Allah yayi musu bushara da Aljjannah, amma Yan Shi,ah karyata hakan, suka nuna tamkar Allah bai ambaci wannanba, Yan Shi,ah suka tuhumi Allah da aikata kuskure da jahiltar wasu abubuwa, Yan Shi,ah suka dauki wasu garuruwa suka daukakasu sama da garuruwan Makkah da Madina suka daukaka wasu Mutane samada Annabawa da Manzannin Allah, kadan kenan daga munananakidun Shi,ah, shin yanzu duk Musulmin kirki mai hankali da Imani zai aminta da cewa Shi,ah Musulunci ce??? Abinda yafi ga duk Musulminda bai karanci akidar Shi,ah ba alittafansu to idan masu bincikowa sun binciko kada ya karyata, kada kuma yayi kokarin jefa kansa ga halaka kamaryadda Yan Shi,ah suka jefa kansu ga halaka maras iyaka ta hanyar nuna cewa suma shi,ahra,ayinsu suke bi, hakika yin hakan jahilci ne, rashin kishin addini ne. Akarshe ina kira ga duk wani Musulmi da ya kasance mai kishin addininsa da nuna tsananiakan duk wani Munafuki mai kokarin chanja da,awar Musulunci da kawo nakasu ga hanyar magabata nagari daga cikin Sahabbai da wanda suka biyo bayansu da kyautatawa. Dafatan Allah ya kiyashemu daga wannan mummunar akida ta Shi,ah Allah ya shiryarda wanda aka yaudaresu bisa Jahilci aka cusa musu wannan muguwar akida, su kuma wanda suke kanta bisa son rai Allah ya maida musu mugun nufinsu, ameen. Just now
Posted on: Fri, 30 Aug 2013 20:08:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015