LA ILAHA ILLAL LAH.Wannan Kalma itace ake kira(1)kalmar - TopicsExpress



          

LA ILAHA ILLAL LAH.Wannan Kalma itace ake kira(1)kalmar shahada,domin itace ke tabbatar da bawa ya shaida babu wanda ya cancanci bauta ta gaskiya sai ALLAH kadai.(2)kalmar tauhidi,domin ita ke tabbatar da ubangiji guda daya ne baya da abokin tarayya ta kowace fuska.(3)kalmar ikhlasi,domin ita ke alamta bawa ya tsarkake ubangijinsa daga mafi girman laifi wato shirka.(4)kalimatul hakk,domin ita ke nuna bawa ya gaskata ubangijinsa guda daya tak ba a hada shi da kowa.(5)urwatul wuthqa,domin ita ke nuna lallai bawa ya rike ubangijin gaskiya wanda shi kadai ne ake yiwa kowane irin nauin bauta.
Posted on: Sat, 16 Nov 2013 16:58:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015