LOKACI: A cikin dukkan rayuwar halittar Ubangiji, babu wani abu - TopicsExpress



          

LOKACI: A cikin dukkan rayuwar halittar Ubangiji, babu wani abu da Allah SWT ya halitta wanda yake tafiya baya tsayawa sai lokaci. Hakika Lokaci shi ne abinda yafi komai muhimmanci a cikin dukkan rayuwar Bani- Adama. A saboda irin Muhimmanci na lokaci Allah ya buga misalai da dama da lokaci a cikin littafinsa mai tsarki (QURAN) Haka kuma, a cikin sura ta 103 Allah SWT da kansa ya yi rantsuwa da lokaci. Wannan kadai ya isa ya nuna mana Muhimmancin lokaci, da yawan mutane da zasu riski saar karshe a rayuwarsa a tambayi me suke so a gidan duniya, babu Shakka karin lokaci za su nema. Sahabbai sun kasance suna yiwa Manzon Allah SAW tambaya game da lokaci (ALKIYAMA) Allah SWT da kansa ya barwa kansa sanin wannan lokacin. Hakika, lokaci yana da matuqar Muhimmancin da ya kamata a bashi kowacce irin kulawa, amma a bayyane ta ke cewar Lokaci bai yi saar iyayan gida ba, sai dai kadan daga cikinmu da suke girmamashi. An haifemu a cikin lokaci, zamu mutu a cikin lokaci, Tabbas LOKACI shi ne abinda zai ga bayan dukkan Bani- Adama gaba dayansu na farkonsu da na karshensu, babu wani mahaluki da zai iya tsayar da lokaci. MU GIRMAMA LOKACI, MU MUTUNTA LOKACI, MU ALKINTA LOKACI. Lallai mu sani Lokaci baya jiran kowa, domin shi matafiyi ne.
Posted on: Tue, 22 Oct 2013 10:55:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015