Labarina ne kuma labarin gaskiya ne , Wato Nasamu kaina acikin - TopicsExpress



          

Labarina ne kuma labarin gaskiya ne , Wato Nasamu kaina acikin tsaka mai wuya, A legos state nake da zama watara nazo ziyara wajen iyayena sai matar yayana ta bani shawara akan me zai hana ta hadani da wata yarinya idan na amince da ita za a hadamu auren family wato dengi ta kara da cewa Fatima yarinya ce mai hankali da kuma imili kuma mai saukin kai ne ga duk abinda aka fada mata naji zuciyata tana bugawa tin kafin naganta nan take na amince da tahadamu sai matar yayana ta kara da cewa kada fa nasata kunya, nace da ita nayi alkawari bazan saki kunya ba, nan take sai ta aikawa Fatima, Fatima ta zo gidan yayana nan take matan yayana ta kirani a waya akan nazo yarinya tana jirani, nayi wanka nashiriya tsab na garzaya zuwa gidan big brother na nayi sallama sukace min nashiga, hakika ban tabba ga macen da tayi min kamarta arayuwata ina nufin ga kyua ga tsawo ga hankali ta gaishe ne na amsa zuciyata ta tafi duniyar tunane ya zanyi na malaketa a matsayin matana nan take na gabatar mata da kaina kuma nace mata Fatima ina neman fili a zuciyarki domin nashuka soyayya na kara da cewa hakika an yaba da halinta da tarbiyarta nan take ta amince dani a matsayin masoyi agareta, muna soyayya har na tsawon shakara daya sonta da kaunarta ya mamaye gurbin zuciyata jini har jijya na kasance idan banji sautin muriyarta to gaskiya ina cikin tashin hankali. Ita kuma tana sona fiye da yadda nake sonta.na tura mahaifa zuwa gidansu mahaifint ya amince sai ga watara kwasam wani dan uwanta yafitto nemanta da aure anche masa anbada ita, da jin haka sai wannan dan uwan nata yaje wajen kakar yarinya nace mata na nema Fatima da aure amma an hana min ita cewa wai anbada ita, nan take ta kira mahaifin yariya da yazo tana son ganinsa, daga zuwansa sai ta kama fada tace idan har baiba wannan GUY yarinya to bazata yafe masa ba, nan take nafara shigan wani hali na damuwa da tunane akan ya zanyi sai dad dina ya kirani ya bani hakuri da na rabu da yarinya ni kuma zuciyata ta kamu da son Fatima ya zan iya yin hakuri da abinda ya kawo min farin ciki arayuwata, bayan kwana biyu sai yarinya tace mu gudu mu bar gari saboda gaskiya idan har ban aure ba to zata shiga wani hali, ni na nuna rashin amincewata da hakan na bata hakuri akan tayi biyeyya ga iyayenta, maganan da nake yanzu tayi aure da wannan dan uwan nan nata hard a yara biyu ni kuma nakasa son wata yarinya har yanzu zuciyata ta makance da son wata mace abin ya kai har na bar Nigeria na koma wata kasa ko zan iya samun wani sauyi amma har yanzu zuciyata batabukatan haka, INA NEMAN TAIMAKO DAGA GAREKU YAN UWANA,,,, NI NAKU MOHAMMED DA SHUWA
Posted on: Wed, 02 Oct 2013 22:04:49 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015