ME YA FARU A KARBALA 24 Labarin Kisan Husaini Ya Game Duniya Da - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 24 Labarin Kisan Husaini Ya Game Duniya Da sauri kuma ba da bata lokaci ba wannan mugun labari ya game duniya. Ana mamaki ya aka yi musulmi mai neman ceton Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya iya kashe jikansa, farin cikin rayuwarsa?! Wannan labari ya mantar da musulmi sauran musibu da fitinun da suka gabata. Daman an ce, ba a jin warin bera idan ana babbakar giwa. A hedikwatar halifanci Sham, Yazidu ya samu wannan labari mai ban mamaki. Sai dai kamar yadda muka fadi a baya, ruwayoyi sun sha banban game da irin tarbon da Yazidu ya yi ma wannan labari. Riwayoyi mafi kusa da gaskiya sune wadanda suka ce, Yazidu ya firgita da jin wannan labari, ya yi tasalima. Sannan ya yi rantsuwa shi bai ce a kashe Husaini ba, kuma bai ji dadin kisan ba. Ya laanci gwamnansa Ubaidullahi, ya ce bai kiyaye alfarmar Manzon Allah ba. Wannan magana ba a cikin littattafan Sunnah kawai ba har a cikin na Shiah akwai ta. Misali, a cikin KITABUL IHTIJAJ na Tabarsi cewa ya yi: A lokacin da aka zo da Ali bin Al Husain wajen Yazid ya ce ma sa, na samu labarin cewa zaka kashe ni. Idan har haka ne, ina son wadannan yan mata (yana nufin kannensa da aka zo da su) ka nemi wanda zai kai su Madina. Sai Yazidu ya ce masa, ai ba wanda zai kai su in ba kai ba. Allah ya laanci Ibnu Murjanah - Ubaidullahi bin Ziyad kenan - wallahi ban sa shi kashe babanka ba. Kuma da ni ne a wurin wallahi ba zan kashe shi ba. Sannan ya yi masa kyauta mai yawa, ya mutunta shi, ya hada shi da yan rakiya tare da sauran matan suka wuce Madina. via Dr. Mansur Sokoto
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 20:15:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015