ME YA FARU A KARBALA 31 Matsayin Malaman Sunna A Kan Wadannan - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 31 Matsayin Malaman Sunna A Kan Wadannan Fitinu Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya sanar da cewa fitinu zasu gudana a bayansa. Kuma ya fadi cewa alherinka yana gwargwadon nisantarka daga gare su. Wadannan hadisai suna nan a shimfide cikin littafan Sunna a Kitabul Fitan na kowane littafi. Duba alal misali: Sahihul Bukhari, Kitabul Fitan, Babun takunu fitnatun al qaidu fi ha khairun minal qaim, Hadisi na 6670. Game da abinda ya faru a Karbala, ba wani sabani a tsakanin malamai cewa, an tafka barna wadda ba ta dace ba. Abin takaici ne da ya nuna cewa ba a mutunta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba a cikin shaanin iyalinsa. Wanda kuwa duk yake da hannu a ciki to, ba abinda zai hana shi gamuwa da fushin Allah in ba tuba ya yi ba tuba ingatacciya. Amma a game da wa ke da alhakin wannan taasa, to kowa ya fadi albarkacin bakinsa. Duk wanda yake da kyakkyawan nazari da sa adalci cikin hukunci zai iya lura da cewa kaddarar Allah ita ce babban jigon abinda ya faru. Kuma duk abinda ka ga Allah ya yi to, tabbas akwai hikima a cikinsa, ko mun san ta ko bamu sani ba. Hasashen da Ibnu Taimiyyah ya yi a nan abin sauraro ne matuka. Ga abinda ya ce: Hasan da Husaini sun rayu a cikin kuruciya zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Don haka ba su samu damar taimaka masa ba a wajen jihadi da yada kalmar Allah kamar yadda sauran sahabbai suka yi. (Misali, ko da aka fara yakin Badar da na Uhud ko auren Nana Fatima da angonta sayyidina Ali (R.A) ba a daura ba). Duk wahalhalun da sahabbai suka sha a Makka da tsangwama da tashin hankali, haka ma duk gwagwarmayar da suka yi bayan sun bar gidajensu da yakokan duk da aka yi; Badar da Uhud da Khandak da Tabuk da sauransu inda Allah ya yi ta rabon darajoji da gafara ga sahabbai (kamar yadda zamu gani a Suratu Ali Imran da Taubah da Ahzab da Fathi dss) su wadannan bayin Allah ba su samu kasancewa a ciki ba. Kasancewar Allah ya zaba masu wani babban matsayi a aljanna ya sa dole ne su ma su fuskanci wasu kalubale da zasu kai ga samun shahadarsu domin daukakar matsayinsu. Don haka ma Ibnu Taimiyyah ya kara da cewa, kashedinka ka zargi Husaini a kan fitowar da ya yi bayan duk shawarwarin da aka ba shi. Ka sani Allah ne yake ingiza shi zuwa ga daukaka da darajar da ya hukunta masa. Duba Minhajus Sunnatin Nabawiyyah na Ibnu Taimiyyah (4/527-536).
Posted on: Sun, 27 Oct 2013 17:48:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015