Mahimman abubuwan da suka faru a Najeriya Shekaru 800 kafin - TopicsExpress



          

Mahimman abubuwan da suka faru a Najeriya Shekaru 800 kafin haihuwar Annabi Isa :Kabilar Nok sun zauna a garin Jos, tun kafin a samu wayewa irinta zamani. Karni na 11 zuwa sama: Aka kafa garuruwa, da masarautu, ciki harda masarautun kasar Hausa data Borno a Arewacin kasar, da masarautun Oyo da Benin a Kudu. 1472– Turawan Potugal suka iso gabar ruwan Najeriya. Karni na 16-18th- Cinkin bayi: An tura miliyoyin ‘yan Najeriya zuwa Amurka a matsayin bayi ta karfi da yaji. 1809– Aka kafa daular musulunci ta Sokoto – karkashin jagoranjcin Sheikh Usman Dan Fodiyo a Arewacin kasar. 1830s-1886– Yakin basasa ya barke a kasar Yarbawa dake kudancin kasar. 1850s– Turawan Burtaniya suka fara kafa matsugunansu a yankin Legas. 1861-1914– Burtaniya ta kara karfafa ikonta kan abinda ta kira yankin Najeriya, ta hanyar mulki ta bayan fage, tare da yin amfani da sarakunan gargajiya a matsayin shugabannin al’umma. 1922– Aka kara wani bangare na kasar Kamaru mallakin Jamus a Najeriya, sakamakon umarnin kungiyar League of Nations. 1960– Samun ‘yancin kai, inda Fira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, ya jogoranci gwamnatin hadin Kan kasa. 1962-63– Kididdigar jama’a mai cike da rudani ta haifar da rikice-rikicen kabilanci da bangaranci. 1966Janairu – aka kashe Abubakar Tafawa Balewa a wani juyin mulki. Inda Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya zama shugaban gwamnatin soji. 1966Juli – Aka kashe Janar Ironsi a wani juyin mulkin na daban, inda aka maye gurbinsa da Lieutenant-Colonel Yakubu Gowon. 1967– Jihohi uku na Gabashin kasar suka balle domin kafa kasar Biafara, abinda ya haifar da yakin basasa. 1970– Shugabannin Biafara suka mika wuya, aka maida yankin zuwa tarayyar Najeriya. 1975– Aka kifar da gwamantin Gowon, sannan ya gudu zuwa Burtaniya, inda aka maye gurbinsa da Brigadiya Murtala Ramat Mohammed, wanda ya fara shirin maida babban birnin kasar zuwa Abuja. Obasanjo – a karon farko 1976– An kashe Mutala Mohammed a wanin juyin mulki da baiyi nasara ba, inda aka maye gurbinsa da mataimakinsa Lieutenant-Jana ral Olusegun Obasanjo, wanda ya taimaka wajen bullo da tsarin shugabanci irin na Amurka. 1979– Aka zabi Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban kasa a wani zabe da aka gudanar na kasa baki daya, wanda ya haifar da jamuhuriya ta biyu. 1983Janairu – gwamnati ta kori dubban daruruwan ‘yan kasashen waje, mafiya yawansu ‘yan kasar Ghana, tana mai cewa sun haura adadin zamansu a kasar, kuma suna tare guraban ayyukan da ‘yan kasar ya kamata su samu. An dai yi Allah wadai da matakin a kasashen waje, amma ya samu karbuwa a cikin gida. 1983Augusta, Satumba – aka sake zabar Shagari a karo na biyu, sai dai an yi zargin tafka magudi. 1983Disamba - Manjo-Janar Muhammad Buhari ya kwaci mulki a wani juyin mulkin da ba’a zubda jini ba. 1985- Ibrahim Babangida ya kwaci mulki a wani juyin mulkin da ba’a zubda jini ba. 1993Juni – Sojoji suka soke zaben shugaban kasa, bayanda sakamako ya nuna cewa Cif Moshood Abiola ne kan gaba wajen lashe zaben. 1993Agusta – aka mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya. Mulkin janar Abacha 1993Nuwamba - Janar Sani Abacha ya kwaci mulki, sannan ya takure ‘yan adawa. 1994– An kama Abiola bayanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa. 1995– aka kashe Ken Saro-Wiwa, ewani mai fafutukar kare hakkin yankin Ogoni bayan wata shari’a da aka yi masa mai cike da suka. A martanin data mayar, tarayyar Turai ta sakawa kasar takunkumi har zuwa shekarar 1998, sannan kungiyar kasashen Commonwealth ta dakatar da Najeriyar. 1998– Allah ya yiwa janar Abacha rasuwa, inda Manjo-Janar Abdulsalami Abubakar ya maye gurbinsa. Yayinda Cif Abiola ya rasu a gidan yari wata guda bayan hakan. 1999– An gudanar da zaben kasa baki daya, sannan aka rantsarda Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kasa bayan ya lashe zaben. 2000– Wasu jihohi sun fara aiki da tsarin shari’ar musulunci a Arewacin kasar duk da rashin amincewar da mabiya wasu addinai suka nuna. Hakan kuma ya haifar da rikice- rikice a sassa da dama. 2001– Rikicin kabilanci a jihar Benue ya haifar da asarar rayuka da dama, tare da raba dubbai da gidajensu. Sannan a watan Oktoba, sojoji suka kashe fararen hula fiye da 200, bayanda aka tura su domin shawo kan matsalar, a wani abu da akewa kallon ramuwar gayya ce bisa sojoji 19 da aka kashe. 2001Oktoba – Shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya, da Mbeki na Afrika ta Kudu da Bouteflika na Aljeriya suka kaddamar da shirin ciyar da nahiyar Afrika gaba wanda aka yiwa lakabi da New Partnership for African Development, ko kuma Nepad, wanda ya kunshi daina yaki domin samun taimako da kuma zuba jari da fitar da kayayyakin da nahiyar ke samarwa. Rikicin kabilanci 2002Fabreru – Kimanin mutane 100 aka kashe a birnin Lagos, a wani rikici da ya barke tsakanin Hausawa da yarbawa. Dubban jama’a ne suka bar gidajensu
Posted on: Mon, 04 Aug 2014 07:57:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015