Mataimakin gwamnan jihar Niger, Alhaji Ahmed Ibeto da wasu masu - TopicsExpress



          

Mataimakin gwamnan jihar Niger, Alhaji Ahmed Ibeto da wasu masu rike da mukaman siyasa 200 a jihar sun sauya sheka daga jamiyyar PDP sun koma APC. Ibeto ne ya sanarda da sauya shekar a filin jirgin sama na garin Minna lokacin da ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC, Janar Muhammadu Buhari. Mataimakin gwamnan ya ce ya sauya sheka ne saboda rashin adalcin da ya ce jamiyyar PDP ta yi masa a zaben fitar da gwani na takarar gwamna a jihar. Ibeto ya ce Mun koma jamiyyar APC saboda an ki yi mana adalci. Kawo yanzu jamiyyar PDP ba ta maida martani ba game da sauya shekar. Wannan matakin zai iya kawo cikas ga jamiyyar PDP mai mulkin jihar wacce ta tsayar da Alhaji Umar Nasko a matsayin dan takararta na kujerar gwamnan a zaben watan gobe.
Posted on: Mon, 19 Jan 2015 16:32:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015