Musha daria Wani mahaukaci ne yasa shadda mai kyau, kamar mai - TopicsExpress



          

Musha daria Wani mahaukaci ne yasa shadda mai kyau, kamar mai hankali ya je daurin aure, sai ya ga wani mai kidan kalangu yana yi wa mutane kirari ana bashi kudi. Sai maukacin nan yace wa mai kalangu ai nima jinin sarauta ne ya kamata ayi min kida, sai mai kalangu da yaransa hankalinsu ya koma kan mahaukacin nan suka rude da kida suna cewa dan sarki jikan sarki. Sai mahaukaci ya ce wa mai kalangu an baka mota yaranka suma an basu mota, sai mai kalangu yace yaushe za muje mu amso? sai mahaukacin yace sai randa kalangu ya fashe. Nan take mai kalangu ya sa wuka duk ya fasa kalangunansa, sai mahaukaci yace shima kalangu an bashi mota mai kalangu yace amma malam baka da hankali ko? sai mahaukacin yace hankali shima an bashi mota, mai kalangu yace malam Allah baka lafiya, mahaukaci yace lafiya itama an bata mota. kuma da kuka karanta wannan labari an baku mota.
Posted on: Sun, 12 Jan 2014 22:44:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015