N I G E R I A WAI -WAYE....... BABBAN LABARI: Gazawar - TopicsExpress



          

N I G E R I A WAI -WAYE....... BABBAN LABARI: Gazawar Jonathan Da Sambo Daga Ashafa Murnai Barkiya Kamar yadda wani masanin kididdiga da binciken yawan jama’a mai suna Basil Davidson ya bayyana, a cikin 1953, wato shekaru sittin ke nan daidai, Nijeriya na da lauyoyi 150 kacal. Yawan likitoci kuma ya ce ba su wuce 160 ba. Gaba dayan yawan al’ummar Nijeriya a lokacin milyan 40 ne, duk a ta bakin Davidson. A ranar da aka bai wa Nijeriya ’yanci daga mulkin Turawa kuwa, Nijeriya na da sojoji dubu takwas kacal. Ranar Talatar da ta gabata ne ta zo daidai da 1 Ga Oktoba, ranar tunawa ko zagayowar ranar da Nijeriya ta samu ’yanci, shekaru 53 baya. Wannan rana, 1 Ga Oktoba, 2013, ta zo ne shekaru sittin daidai da yin wancan lissafi ko kiyasi da Basil Davidson ya yi, kuma ta zo ne a daidai lokacin mulkin mai ci yanzu, Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, wanda ya ci shekaru biyu da rabi na shekaru hudun mulkinsa. Yayin da gwamnati kan yi bukukuwa ko shagulgula domin murnar zagayowar ranar. Su kuma masana da masu fashin bakin al’amurra da kuma mabiya tarihi sau da kafa, sun fi maida hankali ne wajen tattauna abin da baya ta yi, abin da yanzu ka yi da kuma abin da ake hasashe gobe za ta wanzar. A kowace shekara ana waiwaya baya, sai dai kuma a wannan shekarar,wannan rana ta zo a daidai lokacin da babu buk atar tuna bayan, sai dai yin duba ga halin da ranar ta zo ta riske mu, da kuma abubuwan da ke kwance a kasa wadanda mafiya yawan jama’a ke kallon cewa gwamnatin Jonathan ta kasa magancewa. Wasu ma na masu ikirarin cewa a’a, ba kasa magance matsalolin ne Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo suka yi ba, gwamnatin ce ta su gaba daya ta gaza a kowane fanni. Matsalar Tattalin Arziki A daidai zagayowar ranar ’yanci ne ake cike da rudanin tabarbarewar arzikin kasar nan. Yayin da hujjoji bayyanannu ke nuna cewa akwai matsala sosai, gwamnati sai hakikicewa take yi cewa tattalin arziki na nan daram dam dam. Sai dai kuma sabanin da aka samu na kasa biyan jihohi da kananan hukumomin kasafin kudinsu na wannan wata cif-cif, ya nuna cewa akwai matsala sosai, an kudundune ta ne an ki fallasawa. Ba tun yau ba ake zargi da kuma korafin yadda gwamnatin Jonathan ke ragargazar baitulmalin kasar nan, a gefe daya kuma a kullum satar mai sai yawaita take yi tare da yawaitar wuraren tace mai na manyan barayin da ke satar mai suna bumburutunsa zuwa kasashen Turai. Akwai kuma matsalar rashin aiwatar da kasafin kudi wanda abin ya yi muni har kungiyar gwamnonin kasar nan magoya bayan Gwamna Rotimi Amaechi suka yi kira da kakkausar murya ga ministar kudi, Mrs. Ngozi Ikonja-Iweala da ta gaggauta sauka. Ko shakka babu, Jonathan ya harzuka da yawan wadanda suka saurari tattaunawar da aka yi da shi kwanaki biyu kafin ranar tunawa da mulkin kai, inda ya ce cin hanci da rashawa ba su ba ne manyan matsalolin da ke addabar kasar nan. Matsalar Rashin Tsaro Idan akwai inda za a fara ganin gazawar shugaba Jonathan, to tashin farko ita ce wajen matsalar rashin tsaro a kasar nan, wacce a kullum masu adawa na ganin cewa Jonathan ba ya komai sai dai kantara wa al’umma karyar cewa ‘suna kan gabar shawo kan lamarin’, wato ‘we are on top of the situation.’ Shugaba Jonathan ya ba ‘yan Nijeriya mamaki matuka a wata tattaunawa da aka yi da shi, inda ya ce bai sani ba ko har yau Shugaban kungiyar Jama’atu Lid Da’awati Wal Jihad, Abubakar Shekau na da rai ko ba ya da rai ba. Idan ba a manta ba, wata biyu baya, kakakin rundunar JTF a Maiduguri ya bayyana cewa an kashe Shekau. Abin da ya kara bata ran yawancin mutane shi ne, bayan fitowar faifan CD a internet inda Shekau ya tabbatar da cewa bai mutu din ba, babu wanda yayi tababar bayanansa sai rundunar tsaron kasar nan, wadda bayan fitowar CD din ta ce za ta yi nazarinsa tukuna. Sai dai kuma sau biyu yana fitowa yana jawabai bayan sanarwar kisan da JTF din suka ce sun yi masa. Wannan abu ya kunyata rundunar sojojin Nijeriya, kuma ya kunyata gwamnatin tarayya matuka. Masu adawa dai na ganin cewa a kullum gwamnatin Jonathan ta ma daina tafiyar- wahainiya, ta koma yin tafiyar-kura. Shugaba Jonathan ya bar kasar nan zuwa taron majalisar dinkin duniya a birnin New York a daidai lokacin da kurar kisan gillar da jami’an tsaro suka yi a rukunin gidajen kwannan ’yan majalisar tarayya bat a kwanta ba. Sannan ba a dade da kai hari a kauyen Beni-sheik ba, inda aka kashe sama da mutane 140. Kwanaki biyu kafin tattaunawar da aka yi da shi, an yi wa daliban kwalejin koyon aikin gona kisan gilla wanda ya haifar da asarar rayuka kusan casa’in. Kafin wannan, daruruwan mutane sun mutu a daren da aka kona garin Baga. Dukkan wadannan tashe-tashen hankula da kashe-kashe, sun yi tsanani ne daga 2011 zuwa yau. Yayin da ake fama da rikicin Boko Haram a Arewa, a gefe daya kwamitin da gwamnati ta kafa don neman sasantawa, sai gararamba da tarukan shan lemo da shayi kawai yake shiryawa ba tare da ganin cigaba a kasa ba, yawan sojojin da aka jibge a garuruwan Maiduguri da Yobe da kuma wadanda aka kakkafa a sauran yankunan jihohin biyu ba su rage komai ba. Wani abin da ya daure wa jama’a kai shine, a daidai lokacin da gwamnati ke narkar da bilyoyin nairori da sunan tsaro ne matsalar ta fi ta’azzara. Dokar tabacin da aka sa a jihohin biyu dai ba ta da wani tasiri. Kashe- kashen da ake yi a sauran jihohi, musamman kisan dabbanci na matsafan Ombatse a jihar Nassarawa, ya kara nunawa a fili cewa gwamnagtin Jonathan tana da matukar raunin magance matsalar tsaro. Ba don an tashi haikan an matsa wa gwamnatin Jonathan lamba ba, to da ’yan sanda da jami’an SSS sama da saba’in da matsafan Ombatse suka kashe, an kashe kiyashi kenan. Yin ko-oho dangane da maganganun da ’yan kabilarsa ke yi wadanda ke cewa idan ba a bari ya tsaya takara ba za a yi yaki, haka idan ya fadi zabe zaa yi yaki, ta sa da yawan wadanda suka jefa masa kuri’a suna da-na-sani, ganin cewa yana ji, yana gani danginsa na babatu da cika baki suna kalamai masu iya yamutsa kasar nan. Tun bayan harin da su Henry Orka suka kai a Dandalin Eagle Square inda Jonathan ya halarci bikin zagayowar ranar samun mulkin kai cikin 2010, ba’a sake yin bikin a sarari ba. Kamar yadda ya saba, na wannan shekarar shi ma a cikin farfajiyar fadar shugaban kasa aka yi shi. Irin yadda yake nuna tsoro ne a wajen gudanar da wasu abubuwa da suka danganci tsaro ya sa har aka rika yi masa dariya yayin day a ce wa kasar Kenya zai taimaka mata da dabarun dakile ‘yan ta’adda bayan harin da aka kai can kasar a cikin wani katafaren kantin saida kayayyaki, shopping mall. AL-ISL
Posted on: Sat, 05 Oct 2013 23:32:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015