NI KAUNARKA NAKE MAIGIDA ANNABI FARIN CIKIN RAYUWA.KAUNARKA TA - TopicsExpress



          

NI KAUNARKA NAKE MAIGIDA ANNABI FARIN CIKIN RAYUWA.KAUNARKA TA CINYEN ZUCIYA ,BABU KASHI KUMA BA JIJIYA,TABI TA RUHI TA KEWAYA,DUKA GABOBI TA ZAGAYA,DA AMBATONKA NAKE SHAKUWA.NA TAFI BANGA IYAKARKABA,NA NUTSU BANGA MASOMINKABA,BA MAFITA BA HASKENKABA,NI DA FADINKA NAKE YANTUWA.ZANSO KASANI A HASKENKANI,IN BATA BAT BANA GANUWA,ANNABI DAKAI NA NUTSU,NI DA GANINKA KAWAI NA MATSU,KAUNARKA TUNTUNI KAM TA KITSU,A ZUCIYATA TA MARMATSU,BABU ABINDA YAKE KULLUWA.IN NAYI TSIT KAI NE ZAN TUNA ,DANA FADA KAI ZAN BAYYANA,A BINCIKE KAI ZAN AYYANA,SIDI ASHE KAINE KOINA,BABU WANINKA DAKE WANZUWA S.A.W. ALLAH KA KARA NARKAR DAMU A CIKIN BEGEN FIYAYYEN HALITTA,HABEEBY ,MURADY,QALBY WA JASADY,MAULAYA RASULULLAHI S.A.W
Posted on: Wed, 23 Oct 2013 08:23:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015