RASHIN YARDA DA JUNA NA KARUWA TSAKANIN JAMIAN TSORO DA - TopicsExpress



          

RASHIN YARDA DA JUNA NA KARUWA TSAKANIN JAMIAN TSORO DA TALAKAWA. A cikin mako guda tarzoma ta barke tsakanin matasa da jamian yansanda a JEGA ta Jihar KEBBI , da kuma jiya a SHINKAFI da ke jihar Zamfara, wanda hakan ya haddasa asarar rayukan talakawan a rikittan biyu. A Jega dai rikicin ya faro ne bayan matasa sunyi yunkurin fatattakan yansanda daga garin domin a cewarsu wai basuga amfaninsu ba, bayan kisan gillan da wasu da baasan ko suwaye ba sukayiwa wani Attajiri mai taimakon jamaa a garin. A Shinkafi kuwa, an kama wani mutum ne dauke da bindiga samfurin AK 47 da karamar bindiga (pistol) kirar hannu da kuma alburusai sunfi 100 yana shirin zuwa wani daji inda barayin shanu kuma yanfashi suka addabi mutanen yankin, to sai matasa sukayi yunkurin a mikamusu mutumin su zartar masa da hukunci don ba zasu yarda a aike dashi Gusau babban birnin jihar ta Zamfara ba, don sunce an dade ana ruwa kasa tana shanyewa,watau da zarar an aike da masu laifin kwana biyu sai suga an sakosu suna yawonsu. Allah dai ya kyauta, dama indai a cikin jamian tsoro akwai irin su Mr Suleiman Abba to ai babu abinda ba zaka gani ba.
Posted on: Wed, 03 Dec 2014 10:44:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015