Rikicin kungiyar Gwamnoni ya dauki sabon salo Rikicin da ake yi - TopicsExpress



          

Rikicin kungiyar Gwamnoni ya dauki sabon salo Rikicin da ake yi cikin kungiyar Gwamnonin kasar nan ya sake daukar wani sabon sabo, inda barakar da ke cikin kungiyar ya sake fitowa sarari, yayin da a wannan makon bangarorin biyu suka zargi junansu a neman yi wa ci gaban kasar nan kafar ungulu. Barakar da ta kunno kai game da shugabancin kungiyar Gwamnonin ke kara karuwa, bangaren Gwamna Jonah Jang ya kira taron Gwamnonin a ranar Litinin, domin tattauna wasu muhimman batutuwa. Amma bangaren Gwamna Rotimi Amaechi ya ce shi bai san da wani taro ba. Rikicin da ake yi kungiyar Gwamnonin kasar nan ya dauki sabon salo ne, inda Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya umarci sauran Gwamnoni su kauracewa taron da Gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya kira. Gwamna Jang, wanda shi ma yake ikirarin shugabancin kungiyar ya bayyana taron da ya kira a matsayin halatacce. Shi dai Gwamnan na jihar Rivers din ya zargi Gwamna Jonah Jang da neman yi masa ungulu da kan-zabo, wajen ayyana kansa a matsayin Shugaban kungiyar Gwamnonin kasar. A wajen taron da Jang ya kira, Gwamnoni 16 daga cikin 36 ne suka samu halarta, abin da wasu suka bayyana shi a matsayin wanda bai samu nasarar da ake tsammata ba.
Posted on: Tue, 25 Jun 2013 23:10:29 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015