Riwayoyin Hadisin “ITRA” AL KITAB WAL “ITRA” KO AL KITAB - TopicsExpress



          

Riwayoyin Hadisin “ITRA” AL KITAB WAL “ITRA” KO AL KITAB “WAS SUNNAH”? Na (4) Ruwaya ta Farko: Ruwayar sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu wadda Imam Al Baihaki ya zo da ita a cikin SUNAN AL KUBRA (10/144), Hadisi na 20124 da Imam Al Bazzar a cikin MUSNAD (2/479), Hadisi na 8993. Ga nassin Hadisin Abu Huraira: “ ﺍﻧﻲ ﻗﺪ ﺧﻠﻔﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﺛﻨﻴﻦ ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ ﺑﻌﺪﻫﻤﺎ ﺃﺑﺪﺍ: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺘﻲ، ﻭﻟﻦ ﻳﺘﻔﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺤﻮﺽ ”. Fassara: “Hakika na bar maku ababe biyu da ba zaku bace ba idan kun yi riko da su KITABULLAHI WA SUNNATI. Kuma ba zasu taba rabuwa da juna ba har su same ni a tafki (Al Kauthar). Ruwaya ta Biyu: Riwayar sayyidina Amr bin Auf Al Muzani Radiyallahu Anhu wadda Imam Malik ya kawo ta a cikin MUWATTA (1/364), Kitabul Qadr, Babi na daya, Hadisi na 1594, Ibnu Abdil Barr ya fitar da Isnadinta a cikin AT TAMHID (24/331) da AL ISTIDHKAR (8/265) haka shi ma Imam Al Baji a cikin AL MUNTAQA (4/278). ga yadda take: “ ﺗﺮﻛﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﺃﻣﺮﻳﻦ ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ ﻣﺎ ﺗﻤﺴﻜﺘﻢ ﺑﻬﻤﺎ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺔ ﻧﺒﻴﻪ” Fassara: Na bar maku wasu al’amura biyu da ba zaku taba bacewa ba matukar kun yi riko da su: KITABULLAHI WA SANNATU NABBIYIHI. Ruwaya ta Uku: Riwayar sayyidina Zaid bin Thabit Radiyallahu Anhu wadda Imam Muslim ya ruwaito a cikin Sahihin littafinsa, KITABUL FADA’IL, Babi na hudu kan darajojin Ali bin Abi Talib, Hadisi na 6378 da kuma Imam Tirmidhi a cikin SUNAN, KITABUL MANAQIB, Babi na 32 kan darajojin iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam, Hadisi na 3788. Ga ruwayar: “ ﺍﻻ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﺈﻧﻤﺎ ﺑﺸﺮ ﻳﻮﺷﻚ ﺍﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺭﺑﻲ ﻓﺎﺟﻴﺐ ﻭﺍﻧﺎ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺛﻘﻠﻴﻦ: ﺍﺣﺪﻫﻤﺎ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﺍﻟﻨﻮﺭ، ﻓﺨﺬﻭﺍ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺳﺘﻤﺴﻜﻮﺍ ﺑﻪ” ﻓﺤﺚ ﻋﻠﻰ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﻏﺐ ﻓﻴﻪ، ﺛﻢ ﻗﺎﻝ“ :ﻭﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ، ﺃﺫﻛﺮﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ.” ﻗﺎﻝ ﻟﻪ ﺣﺼﻴﻦ: ﻭﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ ﻳﺎ ﺯﻳﺪ؟ ﺃﻟﻴﺲ ﻧﺴﺎﺅﻩ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﺴﺎﺅﻩ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ، ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ ﻣﻦ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺑﻌﺪﻩ. ﻗﺎﻝ: ﻭﻣﻦ ﻫﻢ؟ ﻗﺎﻝ: ﻫﻢ ﺍﻝ ﻋﻠﻲ ﻭﺍﻝ ﻋﻘﻴﻞ ﻭﺍﻝ ﺟﻌﻔﺮ ﻭﺍﻝ ﻋﺒﺎﺱ. ﻗﺎﻝ: ﻛﻞ ﻫﺆﻻﺀ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﻌﻢ . Fassara: “Ya ku mutane, Ku saurara! Ni fa mutum ne da ana kusa manzon ubangijina ya zo min da kira in karba (yana nufin mutuwa). Kuma ni mai bar maku abubuwa biyu ne masu nauyi: Na farkonsu shi ne littafin Allah Wanda akwai shiriya da haske a cikinsa. Don haka, ku kama littafin Allah ku yi riko da shi”. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi WA Alihi Wasallam ya yi ta kwadaitarwa da Jan hankali zuwa ga littafin Allah. Sannan saiya ce: “Da kuma iyalan gidana. Ina taunatar da ku Allah a game da iyalan gidana”. Husain sai ya tambayi Zaid, su wane ne iyalan gidansa? Matansa ba sa cikin iyalan gidansa? Zaid ya ce, suna ciki mana. Amma iyalansa sun hada da duk wadanda aka haramta ma cin zakka a bayansa. Ya ce, su wane ne? Ya ce, su ne dangin Ali, da na Akilu da na Ja’afar da na Abbas. Ya ce, duk wadannan an haramta masu cin zakka? Ya ce, eh. Ruwaya ta Hudu: Ruwayar da Adiyya Al Ufi ya karbo daga Abu Sa’id (Ko dai Abu Sa’id Al Kalbi ko kuma Abu Sa’id Al Khudri). Wannan ruwaya tana cikin MUSNAD na Imam Ahmad bin Hambal, hadisai masu wadannan lambobin: 11119 da 11147. Da kuma MUSNAD na Imam Abu Ya’la (2/1021), Hadisi na 1021. Ga ruwayar: “ ﺍﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺜﻘﻠﻴﻦ ﺍﺣﺪﻫﻤﺎ ﺍﻛﺒﺮ ﻣﻦ ﺍﻻﺧﺮ: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺒﻞ ﻣﻤﺪﻭﺩ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺍﻻﺭﺽ، ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ. ﻭﺍﻧﻬﻤﺎ ﻟﻦ ﻳﻔﺘﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺤﻮﺽ ”. Fassara: “Hakika ni mai barin ababe biyu masu nauyi ne a cikinku. Dayansu ya fi daya nauyi: Littafin Allah da yake igiya ce mikakkiya daga sama zuwa kasa. Da iyalaina. Kuma lalle ba zasu rabu ba har sai sun zo mini a tafki”. Ruwaya ta Biyar: Ruwayar sayyidina Zaid bin Thabit Radiyallahu Anhu wadda Imam Ahmad ya ruwaito a cikin MUSNAD, Hadisi na 21578 da 21654 da Ibnu Abi Shaibah cikin AL MUSANNAF (11/452), Hadisi na 32337. Ga yadda ruwayar take: “ ﺍﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺨﻠﻴﻔﺘﻴﻦ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻱ: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ ﺍﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ، ﻭﺍﻧﻬﻤﺎ ﻟﻦ ﻳﻔﺘﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺤﻮﺽ ”. Fassara: “Hakika ni mai barin halifofi biyu ne a cikinku bayana: littafin Allah da iyalan gidana. Kuma ba zasu rabu ba har sai sun zo mini a tafki. Wadannan su ne riwayoyin Hadisin. Wanne ne ya inganta a cikinsu? Wanne ne bai inganta ba? Kuma saboda me? Sa’annan mene ne Hadisin yake koyarwa? Ina muka yi sabani da ‘yan Shi’a a game da wannan Hadisi? Sai ku dakace mu. Daga DANDALIN AHLULBAITI DA SAHABBAI na DR. MANSUR SOKOTO mansoorsokoto.wordpress
Posted on: Wed, 04 Sep 2013 17:26:32 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015