SOYAYYA KAFIN AURE: KURA CE DA KAN RAGO. Tambayar da wasu ke yi - TopicsExpress



          

SOYAYYA KAFIN AURE: KURA CE DA KAN RAGO. Tambayar da wasu ke yi ita ce, wai ya za a yi ka ga yarinyar da ta kwanta maka a rai, kuma a ce ka kyale ta don ba ka tashi aure ba? To ni kuma sai nake tambayar su, me ya sa za ka ga mota mai kyau, wadda ta kwanta maka a rai, kuma kana matukar sha’awar ta, amma ka bari ta wuce ka? kila don ba ka da kudin sayen ta, ko kuma ba ka tashi sayen motar ba, to ai ita ma mace kamar haka ne, dole ne ka bar ta idan har ba ka tashi aure ba, ko kuma Allah Bai hore maka abin auren ta ba. Abin da ya kamata shi ne, ka roki Allah ya ba ka wadda ta fi ta, kuma ya hore maka abin da za ka yi auren. Idan dai har bariki kake so ka yi, to akwai ‘yan mata da yawa, sai ka je can ku yi barikinku, kafin ranar da Allah Zai karbi rayukanku, ya kuma yi muku hisabi a kan laifukanku. Amma dai, a daina labewa ga aure anayin yaudara. Har ila yau, ya kamata mu gane cewa, tsananin son zuciyar maza ke sa su neman mace ba tare da sun tashi aure ba. Haka kuma shi ne ke sa wa, maza ke ganin tamkar wayewa ce mace da namiji su daidaita kansu a tsakaninsu su kadai. A tawa fahimta, mahaifa ne ya kamata su yi ruwa su yi tsaki a cikin auren ‘ya’yansu. Ban yarda da auren dole ba, haka ma ban yarda da auren sha’awa ba, saboda haka, ba ina nufin a yi wa yara auren dole ba, amma dai a zabar wa yaro yarinyar da aka yarda da kyawawan halayenta da addininta, wadda aka fahimci rayuwarsu tana kan ma’aunin da za su iya zama lafiya. Da ma aikin yaro da yarinya bai wuce gano fuska mai kyawu ba. Daga jin kalaman saurayi ga budurwarsa, ka san akwai kuruciya da rashin sanin makoma a ciki. Wai sai ka ji yana ce mata: “Abin da yake burge ni da ke shi ne, kyawun surar da Allah Ya yi miki, musamman fararen idanuwanki! Masoyiyata, tun ranar da na fara haduwa da ke, takawarki take matukar burge ni! Zubin jikinki ya yi mini daidai. Ga iya kwalliya, ga zakin murya.....” ita kuma, daga jin haka, sai ka ga farin ciki da nishadi ya lullube ta, wai an yabe ta. Jama’a ba haka ake hira ba. To duk abubuwan da ya jero mata din nan, su ne manyan ababen bukata a cikin aure? Kina da halayen kirki, kowa sai yabon dabi’arki yake yi, Allah Ya ba ki karatu da kaifin basira. Babban abin da yake burge ni da ke shi ne, tsananin rikon addininki! Sau nawa ka taba jin saurayi ya yi wa budurwarsa irin wadannan kalamai? To ashe dai idan aka ce yaro ya nema wa kansa aure, abu na farko da yake nema yarinya kyakkyawa. ita kuma budurwa, abin da take dubi ta samu mai kudi, ko wanda ya iya kalaman soyayya. Bisa ga wadannan dalilai, sai muka ce a tuna da baya, shin mahaifa da kakanninmu da suke zaune lafiya a gidajen aure, sun yi irin wannan soyayyar ne? Ba haka suka yi ba. To yaya suka yi? Mahaifansu ne suka zabar musu matan aure, kuma a haka suka zauna lafiya har suka haife mu...... To samari Qalubalen ku.
Posted on: Sun, 07 Jul 2013 09:31:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015