**TASKAR ALKHAIRI** ~~Dolene Ga Kowane Musulmi.... Hakika - TopicsExpress



          

**TASKAR ALKHAIRI** ~~Dolene Ga Kowane Musulmi.... Hakika Alkhairai za su tabbata ga wanda ya bar duniya kafin ta barshi, sanan ya gina kabarinsa kafin ya shige shi, Kana kuma ya yarda da ubangijinsa tun kafin ya hadu dashi. Karin bayani a nan shi ne, ka guji duniya a lokacin da take sonka kuma a lokacin da take son nakane ake son ka nemi ‘yaruwarta wato lahira domin a dai-dai lokacin da zata gujeka, kai kuma kayi mata nisa. A cikin duniya ake neman lahira sannan sakamakon lahira yana farawa ne tun a cikin kabari, kuma yin tanadi domin kwanciyar kabari dole ne ga kowane musulmi, dan haka, danuwa mu kyautata ayyukanmu domin mu riski daddadan sakamako da makwanci kyakkyawa kuma ni’imtacce. Dukkanin wadannan abubuwa da aka lissafa, dan Adam ba zai cinmasuba sai in har ya yarda da ubangijinsa kuma yayi biyayya a gareshi. A karshe Ku sani ya ‘yanuwa musulmai, mutumin kirki baya sabawa Allah kuma duk mai hikima baya fifita duniya akan lahira. Allah yasa mudace…………
Posted on: Sat, 17 Aug 2013 20:57:21 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015