TAUHIDI HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA NA: SHAYKH UMAR MUHAMMAD - TopicsExpress



          

TAUHIDI HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA NA: SHAYKH UMAR MUHAMMAD LABDO Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci Jami’ar Usmanu Dandofiyo, Sakwato MAI RUBUTU: UMMU ABDILLAH ZARIA HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA //07 **TAUHIDIN ULUHIYYAH** Tauhidin Uluhiyya shi ne mutum ya kudure cewa Allah, Shi kadai, Shi ne ILAHU. Ma’anar Ilahu a Larabci shi ne abin bauta, ko kuma wanda ya cancanci a bauta Masa. Allah, Shi kadai, Shi ya cancanci a bauta Masa; Shi ne abin bauta na gaskiya, wanda ake bautawa da cancanta, kuma ba shi da abokin tarayya a cikin Uluhiyyarsa (bautarsa). Tauhidin Uluhiyya ana gina shi a kan Tauhidin Rububiyya: watau tunda Allah, Shi kadai, Shi ne Rabbu wanda ya halicci halitta kuma yake kulawa da ita, to tabbas Shi kadai Shi ya cancanci ya zama Ilahu, watau abin bauta na gaskiya. Wanda ya halicci halitta shi ya kamatahalittu su bauta Masa; shi ke da hakkin a bauta Masa. Idan da halitta za su bautawa waninsa to da sun yi zalunci, domin sun dauki hakkinsa sun baiwa wani wanda bai cancance shi ba. Wannan ya sa ake kiran shirka zalunci kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa, «Kuma a lokacin da Lukman ya ce da dansa, alhali kuwa yana yi masa wa’azi : Ya karamin dana! Kada ka yi shirka game da Allah. Lalle Shirka wani zalunci ne mai girma» [Suratul Lukman : 13]. Dangane da Tauhidin Uluhiyya, Allah yana fadi a cikin littafinSa mai tsarki, «Kuma abin bautawarku abin bauta ne guda. Babu wani abin bauta face Shi, Mai rahama Mai jin kai» [Suratul Bakara : 167]. Kuma Yana cewa, «Shi ne Allah babu abin bautwa face Shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai kamun kai. Tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirka da Shi » [Suratul Hashr: 23]. Har yau, Yana fadin, « Lalle Ni, Ni ne Allah. Babu abin bautawa face Ni. Sai ka bauta Mini kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni» [Suratul D.H : 14]. Har ila yau, yana cikin Tauhidin Uluhiyya kadaita Allah da hakkin umurni da hani, da halattawa da haramtawa, da sanya shari’a, da aza doka, da tsara rayuwa. Duka wannan hakkinsa ne a matsayinsa na Rabbu. Tunda Shi kadai shi ya halicci halitta, to, Shi kadai yake da hakkin da zai umarce su ko ya hana su; Shi ka halatta musu ko ya haramta musu; kuma Shi kadai yake da hakkin ya tsara musu rayuwarsu (domin shi ya ba su rayuwar) kuma su bi a tsarinsa sau da kafa. Haka kuma yana cikin Tauhidin Uluhiyya kadaita Allah da dukkan nau’o’in ibada da launukanta. Ibada tana da nau’i hudu : (1) Ibadar zuciya, kamar son Allah da tsoronSa da dogaro a gare Shi da girmama Shi da fatar rahamarSa, da sauransu. (2) Ibadar harshe, kamar zikiri da yabon Allah da gode masa da tsarkake shi da yi masa kirari da neman gafarasa (istigfari) da rokon sa (addu’a) da neman tsanantuwa gare shi (tawassuli) da neman tanyonsa (istigasa), da abinda ya yi kama da haka. (3) Ibadar gabobi, kamar Sallah da Azumi da Dawafi da Jihadi. (4) Ibadar dukiya, kamar Zakkah da Sadakka da ciyarwa, da sauransu. Duka wadannan nau’o’i hudu na Ibada hakkin Allah ne Shi daya, bai halasta a fuskantar da wani abu daga cikinsu zuwa ga waninsu. In sha Allah, zamu ji na uku kuma na karshe cikin kashe kashen Tauhidi wanda yake da faddadan bayanai, wato "TAUHIDIN SUNAYE DA SIFOFI," duk a cikin littafin TAUHIDI “HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA” na Shaykh Umar Muhammad Labdo, Allah Ya saka mai da alkhairi.
Posted on: Sat, 31 Aug 2013 12:16:48 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015