¤¤¤¤¤ Tambayoyi Da Amsar su tare da Sayyed Ibraheem - TopicsExpress



          

¤¤¤¤¤ Tambayoyi Da Amsar su tare da Sayyed Ibraheem Zakzaky ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤ TAMBAYA ¤¤¤¤¤ :~ Allah ya gafarta Malam, wasannin tashe da ake yi idan azumi ya kai kwana goma, menene asalinsa, kuma ya matsayinsa a Musulunci? ¤¤¤¤¤ AMSA ¤¤¤¤¤ :~ Al’ada ce dai kawai. Kuma abin mamaki kusan ko’ina a kasashen musulmi suna wannan al’ada din, yakan bambanta tsakanin wannan wuri da wannan wuri, kasashen Larabawa suna yi, wasu wurare ya zama zaunennan abu, mai yiwuwa saboda yanayin rayuwa irin ta da mutanen da, da duhu, da kuma sai an ta da mutane. Amma kuma yanzu ya zama kawai wasannin ne, ba a bukatar sa. Amma a da ana bukatar sa sosai don a tashi mutane su dafa abinci, amma yanzu ba a bukata, saboda mutane suna da agogwanni masu karaurawa, da kuma yanzu ma daren ma ba a cika barci sosai ba. Amma dai al’adar mutane ne, kuma ba laifi da shi, tun da ba an ce aibada ne da aka ruwaito ana yi ba. Al’ada ce kuma ba ta yi karo da shari’a ba, saboda haka ba komai. Allahumma sai dai in akwai wasu abubuwa da ake yi a tashen, wanda ya saba ma shari’a, sai a ce to su a bar su. Amma shi tashe a kashin kansa kawai al’adar mutane ne. ¤¤¤¤¤ TAMBAYA ¤¤¤¤¤ :~ Allah gafarta Malam ko zan iya karatun Kur’ani a cikin sujada a sallar nafila? ¤¤¤¤¤ AMSA ¤¤¤¤¤ :~ A’a, ba a karanta Alkur’ani a ruku’u da sujuda, sai dai in wani bangare nasa da ya bullo da unwanin addu’a, kamar ‘rabbana atina fiddunya hasana’, ko abin da ya yi kama da haka nan, amma ba matsayin kira’a ba. Kira’a a tsaye ake yi, amma ba a yi a sauran wurare. ¤¤¤¤¤ TAMBAYA ¤¤¤¤¤ :~ Allah ya gafarta Malam, an ce balagar ’ya mace shekara 10, namiji kuma shekara 14. Tambayata ita ce, ‘ya ta shekararta 10, amma kuma azumi na ba ta wahala, ita da dan uwanta. Shin Malam me ya kamata in yi? ¤¤¤¤¤ AMSA ¤¤¤¤¤ :~ To, na farko dai ba a ce shekara 10 ba ne, 9 ne ma, bai kai 10 ba, ga ’ya mace. Shi kuma namiji yakan zama galiban 12 ne. Yanzu muna ganin abubuwa na sassakewa na yanayin jikkunan yara din, wala’alla shi ya zo a rubuce haka nan. Don da mu mun saba yara din ba sukan balaga ba, kamar maza, sukan kai 17 a da can, mata kuma sukan kai 14, amma sai muka ga yanzu balagar tasu tana komowa baya, wala’alla shi ya sa shari’a ta zo da shi don ta san zai kai haka nan. To, idan yarinya ba za ta iya azumi ba, to sai a dauki wadansu matakin da za a iya saukaka mata, kamar misali a kirkiri tafiya. Amma dai lallai matukar tana nan, azumin ya hau kanta. Sai dai ni ina ganin wannan rashin iyawar, kila har da rashin tarbiyyantar da yaran su yi azumi tunda wuri. Tunda mu yaranmu nan, ba su shan azumin tun kasa da shekara 7, suna Ramadan din su cikakke, kuma har su kai balaga din. Amma lallai in har ba za ta iya ba, to lallai kuma ya hau kanta. Saboda haka sai dai a bi wata hanya ta shari’a, alal misali tafiya. Sai a kirkiri tafiyar da zai ja mata ta sha, har a jira in kafin wani Ramadan za ta yi azumi, sai ta rama. ¤¤¤¤¤ TAMBAYA ¤¤¤¤¤ :~ Mutum ne ya wayi gari da janaba a watan Ramadan. Ina matsayin azuminsa na wannan rana? ¤¤¤¤¤ AMSA ¤¤¤¤¤ :~ To, idan ba bisa sakensa ne ya sa ya kwana da janabar ba, kamar alal misali, barci ne ya rinjaye shi, sai gab da ketowar alfijir sai ya yi mafarki, misali. Amma banda kamar a ce shi ya sabbaba ma kansa janaba din, kamar ta hanyar saduwa da iyali, sai ya ga dama ya kwanta kafin alfijir, sai alfijir ya keto, ka ga wannan da gangan kenan. Wato wannan tambayar da yake yi, za mu iya cewa kamar ba shi ne ya sabbaba ma kansa ba, tunda shi bai gaya mana yadda janabar ta samu ba. In ba shi ne ya yi sake ba, ya zama gari ya waye masa da janaba din ba, to sai ya zama ramuwar wannan azumin ne kawai ya hau kansa. In da sake a nasa bangaren. Alal misali ya san da janabar, ya wayi gari da ita, ko ya yi gangancin yin barci gab da ketowar alfijir, to lallai ramuwa da kaffara ne a kansa. ¤¤¤¤¤ TAMBAYA ¤¤¤¤¤ :~ Allah gafarta Malam, ko mai kasaru zai iya jan mazaunin gida salla, haka shi ma mazaunin gida ya ja mai kasaru? ¤¤¤¤¤ AMSA ¤¤¤¤¤ :~ In na fahimci abin da yake nufi, yana iya zama Liman kenan, ko kuma daya yana iya koyi da daya kenan. Mai kasaru zai iya bin mai cika salla, haka ma mai cika salla zai iya bin mai kasaru, amma kowa zai bi sunnar da ta hau kansa. Wato mai kasaru, ya yi kasaru, mai cikawa ya cika sallarsa. Idan mai cikawa ya bi mai kasaru, in mai kasaru ya gama nasa sai ya cika. Idan mai kasaru ya bi mai cikawa, in mai cikawan ya yi raka’a biyu, yana iya sallamewa.
Posted on: Thu, 28 Nov 2013 21:14:02 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015