WANE NE BAHAUSHE?? Tare da Abdulwahab Sani Daniya Sanin ko - TopicsExpress



          

WANE NE BAHAUSHE?? Tare da Abdulwahab Sani Daniya Sanin ko wane ne Bahaushe yana da mutukar wuya, shi yasa masana da dama suka tofa albarkacin bakinsu a kan wane ne Bahaushe? Suka kuma kafa hujjoji mabambanta, maana kowane hujjarsa ta bambanta da ta dan uwansa, amma idan aka duba hujjojinsu zaa fahimci cewa raayoyinsu sun bambanta kamar haka:- * masu raayin addini * masu raayin siyasa masu raayin zamantakewa * masu raayin harshe/alada 1- MASU RAAYIN ADDINI masu wannan raayi suna ganin cewa Bahaushe shin wanda musulmi ne, kuma uwarsa da ubansa musulmai ne, yana kuma zaune a kasar Hausa. Masu wannan raayi na ganin cewa lokacin da addinin Musulunci ya zo a kasar Hausa gaba daya Hausawa suka musulunta, sai fa yan tsiraru daga cikinsu, shi yasa ma suke kiransu da Maguzawa, idan suka ce Bamaguje suna nufin wanda bai amshi musulunci ba. Saboda haka suke ganin cewa idan har baka cika wadannan sharudda ba, ba zaa kiraka Bahaushe ba. Anan zan dakata sai jibi zan kawo muku hujjojin sauran masana a kan wane ne Bahaushe amma kafin nan me zaku ce a kan wannan raayi na addini?
Posted on: Sat, 02 Nov 2013 18:35:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015