WANI AZZALUMIN SARKI YAYI NADAMA! Wata rana wani azzalumin sarki - TopicsExpress



          

WANI AZZALUMIN SARKI YAYI NADAMA! Wata rana wani azzalumin sarki ya na zaune a karagar mulkinsa yana taqama yana hura hanci sai kace wani bijimin sa, yana zaune sai wani Quda ya hau kan fuskarsa sai ya sa hannu ya kore shi. Sai Qudan ya sake dawowa a karo na biyu ya sake sauka akan fuskarsa sai ya sake korarsa. Sai Qudan ya sake dawowa a karo na uku, nan ma dai ya kai masa duka da hannu. Haka dai su kai ta yi da kudan nan tsawon lokaci... Sam Qudan ya hana shi sakat... Yayi- yayi ya kashe kudan ya kasa. Da abin ya dami Sarkin sai ya kira wani malami mai suna DAHHAK ya ce masa: Wai me yasa Allah Ya halicci wannan kudan ne? Sam ni banga amfanin hallitarsa ba. Nan take sai Malamin ya ba shi amsa kamar haka: Ya ce Ai shi wannan kwaron an hallice shine domin ya nuna ma azzalumai irin ku cewa ku ba komai bane, baku da iko akan sa. Dubi yadda kake azabtar da mutane, kana sa su aikata abinda ka gadama, amma ga shi dan karamin kwaro yaki yima ladabi, zai je ya hau kazanta sannan ya dawo ya hau kan fuskarka. Idan da ka fahimci abinda kwaron nan yake cema to shine: Kai ba komai bane, ka iya mulkar duniya amma ni ba zaka iya mulkata ba. Ka sani cewa idan Allah yaso zai iya hallakar da kai kamar yadda ya hallakar da LAMARUDU da dan karamin sauro. Tunda Sarkin nan ya ji haka sai yayi nadama, ya bar zaluncin da yake yi a da, ya gane cewa lallai Allah ne kadai ke da mulkin komai. ABIN LURA ANAN SHINE: -Ka sani cewa komai zaluncin azzalumi tofa bai fi karfin Allah ba. -Ka da ka damu, karshen azzalumi dai nadama ce da kaskanci. -Duk lokacin da azzalumi ya tsananta zalunci a kan ka, to kai kuma ka tsananta addua akan sa domin Allah yana karbar adduar wanda aka zalunta cikin gaggawa. A duk lokacin da na karanta labarin nan, sai naji Imani na ya karu, domin waazi ne babba, kuma bana gajiya da karanta shi, kai fa? Yaa Allah! muna rokon Ka, Kai mana maganin azzalumi duk inda yake a fadin duniya. Yaa Allah! Ka gyara mana Arewarmu, ka kawo zaman lafiya mai dorewa.
Posted on: Wed, 13 Nov 2013 15:05:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015