Wani Babarbare ne ya zo wucewa sai ya ga wata motar ’yan sanda - TopicsExpress



          

Wani Babarbare ne ya zo wucewa sai ya ga wata motar ’yan sanda tana dauke da ’yan fashi da aka yanke wa hukuncin kisa. Shi kuma saboda neman banza sai ya tsayar da ita wai a rage masa hanya. Aka tsaya ya shiga, duk inda aka tsaya a hanya, sai a ce dan fashi daya ya fito. Yana fitowa kuwa sai a harbe shi. Haka aka yi ta yi har ya rage saura Babarbare kadai. Da aka zo wani wuri sai aka ce ya fito shi ma. Shi kuwa sai ido ya raina fata, ya ce: “Wallahi ni ba zan fito daga motar nan ba sai an kai ni gaban Sarkin Borno.
Posted on: Thu, 05 Sep 2013 12:26:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015