Wani Dattijo ne yake mura, sai yazo wajen wani mai kanti neman - TopicsExpress



          

Wani Dattijo ne yake mura, sai yazo wajen wani mai kanti neman ROBB, mai kanti yace babu. Dattijo yace to Mentholatum fa? Mai kanti yace duk babu sai LOKO kuma shi zafi gare shi sosai Dattijo yace Kai yaro wani zafi? Mu da muke shaka TEAR GAS idan muna mura a lokacin da nake soja. Mai kanti ya dauko masa LOKO ya bashi. Nan take dattijo ya lakato ya tura a hancinsa, ya kara lakatowa ya tura a dayan. Kafin mai kanti ya kawo canji Dattijo ya fara tsalle saboda azabar da yake ji. Dattijo ya waiwayo kan me kanti yace kai yaro, duba min ka gani Hanci na yana nan? Mai kanti yace Eh mana baba, yana nan. Dattijo yace To amma feshin wuta yake ko? Mai kanti ya fashe da dariya yace Aa baba!!!
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 21:34:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015