Wani gaye ne yaje gidan su budurwarsa da sallah domin ya gaida - TopicsExpress



          

Wani gaye ne yaje gidan su budurwarsa da sallah domin ya gaida iyayanta aka kaishi daki bayan ankawo masa abinci ya cika cikinshi taf sai aka kawo masa wani soyayyan nama naman yayi kyau sosai kuma yaga bazai iya hakura ba, kawai sai ya cire hularsa ya zuba naman aciki ya maida hularsa akanshi, can sai budurwar tashigo dakin yace mata shi zai tafi sai suka fito tsakar gida taje ta kira iyayanta cewa ibrahim zai tafi su fito suyi sallama babarta da kishiyarta da kannanta duk suka fito suga saurayin walida, shi kuma ya durkusa irin ladabinnan, bayan sun gama sallama ya mike tsaye kenan sai igiyar shanya ta rike hular kawai sai ga nama ya baje akasa agaban mutanan gidan.... Wai in kaine saurayin ya zakai??? In kece walida ya zaki??? Barkanmu da sallah...
Posted on: Thu, 08 Aug 2013 16:59:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015