Wasu samari ne guda biyu abokan juna, dayan yayi karatun boko, - TopicsExpress



          

Wasu samari ne guda biyu abokan juna, dayan yayi karatun boko, shi kuma dayan baiyi ba... Wata rana suna zaune a bakin hanya, sai sukaga wata kyakkyawar yarinyar ta taso daga makarantar boko tana rike da littafai a hannunta. Sai wannan saurayin da bai yi karatun # bokoba yaji yana son yarinyar, yana son ya tsayarda ita amma kuma yana tsoro, sai ya tambayi abokinsa wanda yayi karatun boko akan idan yaje wajanta mai zai fada mata da turanci! Abokin yace, in kaje farko ka ce ma ta HELLO in ta amsa sai kace ma ta SLAP ME PLEASE! ko me tace maka kace ma ta YES!!.. Haba! Nan fa gayen ya tashi yana kwambo ya yi wajan yarinyar abokin yana taka mai baya, ga nan yanda hirar su ta kasance: Saurayi: Hello! (yana murmushi yana kwambo) budurwa: Hy! Saurayi: Slap me please! Budurwa: Slap ??? Saurayi: Yes!! Budurwar nan saida ta dage ta zafga mai mari a fuska. Ya dape fuskar sa ya juyo wajan abokinsa ya ce masa Mari na fa tayi shi kuma abokin sai yayi murmushi yace: turancin yafi karfinta ne, ta kasa gane me kake nupi, yanzu ka ce ma ta SLAP ME AGAIN... Gayen ka sai ya juyo wajan budurwa ya ce: Slap me Again!! Ita ko ta sake sharara masa mari, cikin fushin ya juyo ga abokinsa yace: Babaa, anya tanajin turancin kuwaa?? Shi kuma abokin sai yace: burga take mana, ba turancin da ta iya, sokuwa ce! ya kama hannun abokin suka juya suka tafi... Wai in kaine saurayin da aka mara ya zakayi da abokin nan naka??
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 15:41:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015