ZAUREN FIQHU Malam don Allah ka taimakeni kayi min cikakken - TopicsExpress



          

ZAUREN FIQHU Malam don Allah ka taimakeni kayi min cikakken bayani akan bambance-bamban cen dake tsakanin different discharges dake fita daga alaurar mata (maziyyi, maniyyi, wadiyyi, da sauransu). Wadanne ne suke bukatar wankan janaba? Wadanne ne suke bukatar sabunta alwalla kawai ? Wadanne ne kuma fitowarsu baya bukatar canza alwalla ? Na dade inayin tambayar nan, amma amsoshin basu fahimtar dani ba. Kai kuma naga kana comprehensive bayani, qila idan kayimin zan gane in shaa Allah. (daga wata baiwar Allah) AMSA ****** Wa alaikumus salam. Wannan tambayar tana da muhimmanci sosai. Kuma INSHA ALLAHU zanyi miki bayani cikakke yadda zaki gamsu. {1}. MANIYYI: shi wannan fari ne kuma yana da yauki sai dai baikai na Maza kauri ba.. Yana fitane alokacin kololuwar motsuwar shaawa. Kuma yana tunkudar junansa alokacin fitarsa. Akanji mutuwar jiki da kuma gumi bayan fitarsa. Kuma yana WAJABTA WANKA indai yafita tare dajin dadi afarke ko abacci. {2}. MAZIYYI: shi wani ruwa ne tsinkakke garai-garai yake kamar ruwan sha, yana fitowane a farkon lokacin da shaawar mutum ta motsa ta dalilin tunanin jimaI, ko kallo irin na shaawa, ko rungumar juna, etc. Yana karya alwala. Yana karya azumi (abisa mazhabin Imamu Malik). Kuma anayin tsarkinsane ta hanyar wankewa farjin gaba dayansa. Kuma ya wajaba awankeshi daga jikin tufafi, saboda shi Najasa ne. {3}. WADIYYI: shi wannan wani ruwane mai kauri wanda yake fita akarshen fitsarin mutum. Ko kuma ta dalilin rashin lafiya. Baya wajabta wanka. Kuma hukuncinsu dayane da fitsarin. {4}. DANSHI: shi wannan yana fitane ta farjin mace, daga lokaci zuwa lokaci. Batare da motsawar shaawa ba. Kuma akwai bambanci daga mace zuwa mace. Amma yafi fitowa musamman alokacin da mace take dauke da juna biyu. Wata nata yana zuwa mata yellowish haka. Wata kuma Jaja-jaja. Wata kuma fari fat!! Akwai sabanin Malamai dangane da hukuncinsa, kamar haka: A). Wasu malaman suka ce najasa ne, kuma yana karya alwala. Wannan rarraunar magana ce. Domin kuwa basu da hujja daga littafin Allah ko hadisi ingantacce. Ibnu Hazmin (rah) yace wannan danshin mai tsarki ne. Kuma baya karya alwala. C). Imamu Ahmad da Abu hanifah da Shafiiy sunce wannan danshin mai tsarki ne. Kuma ba zaa wanke tufafin da ya taba ba. (Kamar yadda Ibn Al-Uthaymeen yafada acikin SHARHUL-MUMTIY juzuI na farko, shafi na 396). Sannan idan aka leka cikin ALMAJMUA na Imamun Nawawy (juzuI na farko, shafi na 406) da kuma ALMUGNEE na Imam Ibnu Qudaamah (juzuI na biyu shafi na 88). zaa ga cewar mafiya rinjayen Malamai sun tafi akan haka. Kuma sunce duk da cewar yana da tsarki, amma kuma yana karya alwala. Amma duk da haka akwai kuma wasu Maluman da suka raunana wannan raayin da cewar bai kamata ace wannan ruwan danshin yana karya alwala ba. Dogaronsu anan shine: babu wata hujjah daga Alkurani ko Sunnah akan haka. Sai dai anyi Qiyasi ne na Malamai. Sannan kuma wannan danshin abu ne wanda yake fitowa mace sakamakon niimar da take tare dashi. Bawai ta dalilin motsawar shaawa ko wata cuta ba. Don haka idan akace yana karya alwala, to tabbas mafiya yawan mata ba zasu iya zama ba alwala ba kenan. Qarin bayanin da zanyi akan wannan shine: Idan danshin bai kai yakawo ba, to wannan babu komai. Idan kuwa yana fitane daga lokaci zuwa lokaci, to hukuncinsu daya da fitsari. Idan yafito mata koda tana cikin sallah to alwalarta ta karye. Amma idan ya zamto yana fitane akai akai, kuma da yawa to yazama wajibi mace ta sake yin tsarki da alwala kafin kowacce sallah. Kuma koda tana cikin sallah don ya zubo babu komai. (Hukuncinsa yazama kamar na tasalsuli kenan). Haka Bin Baaz ya fada acikin Majmuul Fatawansa (juzuI na 10 shafi na 130) Don karin bayani dai aleka cikin MAJMUUL FATAWA na IBnu UTHAYMEEN juzuI na 11 shafi na 285-287. {5}. Amma abinda yake fita ta farjin Mace: Musamman wacce take dauke da ciwon sanyi ko wata chutar mahaifa, wanda yake da wari ko doyi kamar gyambo, to wannan najasa ne kuma yana karya alwala. Hukuncinsa kamar na ruwan gyambo ne idan ya taba tufafi sai an wanke shi. Ina fatan kin gamsu. Wallahu aalam Dan Allah Kudinga yin like da comment ko kuma kuyi share dinsa domin kusami ladan wadansu su amfana.
Posted on: Sun, 27 Oct 2013 16:00:09 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015