(s5h3) Imam Ali (a.s) yana cewa: by (SHN) إنّ أحسن - TopicsExpress



          

(s5h3) Imam Ali (a.s) yana cewa: by (SHN) إنّ أحسن ما يألف به الناس قلوب اودّائهم ونفوا به الضّغن عن قلوب أعدائهم حسن البشر عند لقائهم والتفقد في غيبتهم والبشاشة بهم عند حضورهم Lalle mafi kyawun abin da mutane za su yi amfani da shi wajen kwantar da zukatan masoyansu da kawar da kiyayya daga zukatan makiyansu shi ne kyakkyawar tarba gare su yayin da suka hadu da neman yadda suke a lokacin da saduwa ta yi wuya a tsakaninsu da kuma sakin fuska gare su a yayin da ake tare waje guda. (Tuhaful- Ukul shafi na 218). Sakin fuska da faraa da iya cudanya da mutane matakai ne da suke janyo soyayya a tsakanin mutane da hada zukatansu waje guda. Ya zo cikin ruwaya cewa: Nuna kauna rabin hankali ne. Wannan hadisi yana da muhimmancin gaske ga dukkanin jamiai a hukuma ta Musulunci musamman ma malaman da suke kula da maaikatu da cibiyoyi. Saboda maaikata da jamiai dake gudanar da aiki a maaikatu ko cibiyoyi ba su zama daya ba matakin imaninsu, sau da dama halin sanyaya gwiwa ko nuna rashi kula gare su zai iya sanadiyyar taba addininsu da raunana imaninsu. Haka nan kuma sabanin hakan idan aka samu wata kyakkyawar dabia (daga wajen wani jamii) zai yi sanadiyyar janyo mutum ga addini da riko da shi gami da kyakkyawar fata ga Musulunci. Domin mumini faraarsa a fuskarsa take, bakin cikinsa kuwa a zuciyarsa.
Posted on: Wed, 30 Oct 2013 17:03:24 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015