2014, KADAN DAGA CIKIN MANYAN ABEBADAN DA SUKA FARU DAGA FARKON - TopicsExpress



          

2014, KADAN DAGA CIKIN MANYAN ABEBADAN DA SUKA FARU DAGA FARKON SHEKARAR ZUWA KARSHENTA 1. Wasu yan bindiga sun kashe Shehin Malaminnan wato Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, da matarsa da yayansa uku. 2. An gudanar da taron kasa a Abuja domin sharewa Jonathan hanyar tazarce. 3. An kai harin BAM a tashar NYANYA kusa da garin Abuja, mutane da dama sun rasa rayukansu. 4. An sace yan Matan Makarantan Chibok kusan 220 wanda har izuwa yanzu shiru kake ji. 5. Yan majalisan jihar Adamawa sun tsige Murtala Nyako a matsayin gwamnan. 6. Matasa da dama sun rasa rayukansu a wani turmitsitsi wajen daukan maaikata (Immigration). 7. An kai munanan hare-hare a Makarantu biyu a jihar Yobe, Buni Yadi da Pataskun. 8. Wata cutar mai suna Ebola ta shigo Nigeria, yayinda Mutane da dama sun rasa rayukansu. 9. Sarakunan Gwoza da Gombe sun rasu. 10. Jonathan ya dakatar da gwamnan Babban Bankin Nigeria, Malam Sanusi Lamido Sanusi daga mukaminsa. 11. Allah ya amshi ran Sarkin Kano Ado Bayaro. 12. An rantsar da Malam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Sarkin Kano. 13. An kashe yayan Sheikh Ibrahin Elzakzaky guda uku a Zaria tareda wasu almajiransa guda 33. 14. Wani bature ya zargi wasu yan Nigeria da taimakawa BOKO HARAM (SAS da IHIJIRKA). 15. Boko Haram ta kwace wasu garuruwa daga hannun Sojojin Nigeria. 16. Gwamnatin Nigeria ta kashe Ustaz Abubakar Shekau a garin KWANDUGA karo na hudu. 17. POLICE sun hana kakakin Majalisa (Aminu Tambuwal) shiga zauren taro, inda suka harba masu borkonon tsohuwa. 18. An kai harin BAM a Masallacin Jummaa na Sarkin Kano. 19. Kaduna, an kaiwa General Muhammadu Buhari da Sheikh Dahiru Usman Bauchi harin BAM a Kaduna cikin watan RAMADAN. 20. Allah yayiwa Rabilu Musa Ibro rasuwa. 21. Farashin MAN FETIR ya fadi a duniya. 22. Gwamnonin APC bakwai sun koma PDP tawariyya. 23. Gwamnoni biyar na PDP sun koma APC, wanda suka hada da: gwamnan Rivers, da Kano, da Sokoto, da Adamawa da Kwara. 24. Yan majalisu sunki yarda da karin dokar ta baci a jihohin Borno, da Yobe da Adamawa. 25. Ustaz Abubakar Shekau ya bayyana yan Izala, da darikun Tijjaniyya da Kadiriyya da Shia a matsayin Arna, kuma yace yana farautansu. 26. General Buhari ya lashe zaben fidda gwanin jamiyyar APC. 27. Anyi barazanar tsige gwamnan Nasarawa Tanko Almakura. 28. Tambuwal yayi tambul cikin APC. 29. Shekarau da Bafarawa sunyi tsalle cikin PDP. 30. Rubuta wanda bam rubutaba da kanka.
Posted on: Thu, 01 Jan 2015 07:27:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015