ABIN ALAJABI: Idanuwan Dattijuwa Sun Bude Bayan Shekaru 7 A - TopicsExpress



          

ABIN ALAJABI: Idanuwan Dattijuwa Sun Bude Bayan Shekaru 7 A Lokacin Aikin Hajji Wata dattijuwa yan kasar Sudan wanda ta rasa idanuwanta kusan shekaru bakwai da suka gabata, ta ci gaba da gani tangararan, kwanaki kadan bayan ta ziyarci kasar Saudiyya domin sauke farali. Dattijuwar mai suna Fatima Al-Malhi, ta bayyana cewa an yi mata aiki a idon sau da dama tun bayan da ta daina gani amma ba ta samu lafiya ba, sai bayan da ta je aikin hajji ta roki Allah ya ba ta lafiyar idanuwan na ta. Na shafe kwanaki a masallacin Harami ina rokon Allah ya ba ni lafiya, cikin ikonsa yanzu ina iya ganin komai, na ga dana a karo na farko cikin shekaru bakwai, yanzu zan iya zuwa ko ina ba tare da taimakon kowa ba - a cewar Fatima lokacin da jaridar Okza ta kasar Saudiyya ke tattaunawa da ita.
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 18:04:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015