ABUBUWA UKU NE SUKE BIN MAMACI SAI BIYU SU DAWO DAYA YA ZAUNA TARE - TopicsExpress



          

ABUBUWA UKU NE SUKE BIN MAMACI SAI BIYU SU DAWO DAYA YA ZAUNA TARE DASHI Anas dan Malik Allah ya qara yarda a gareshi yace : "Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Abubuwa ukune suke bin mamaci, sai biyu su dawo, sai daya ya zauna tare da mamacin. Iyalansa da dukiyarsa da aikinsa zasu bishi, sai Iyalansa da dukiyarsa su dawo, sai aikinsa ya zauna tare da shi“. [Bukhari da Muslim suka ruwaito]. Duk wani abu da dan Adam zai tara to tabbas a duniya zai barshi, yanda yazo duniya babu komai haka zai koma. Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤَﺎﺕِ ﻟَﻨُﺒَﻮِّﺋَﻨَّﻪﻡُ ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﻏُﺮَﻓًﺎ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﻣِﻦ ﺗَﺤْﺘِﻬَﺎ ﺍﻟْﺄَﻧْﻬَﺎﺭُ ﺧَﺎﻟِﺪِﻳﻦَ ﻓِﻴﻬَﺎ ۚ ﻧِﻌْﻢَ ﺃَﺟْﺮُ ﺍﻟْﻌَﺎﻣِﻠِﻴﻦَ "Kuma wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle za Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidajen bene, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon masu aikin ƙwarai". Allah kasa mu zama masu aikata ayyukan kwarai, Allah kuma yasa mu kasance daga cikin masu gadon Aljannah Firdausi. KUYI #SHARE DA #LIKE DA #COMMENT DOMIN ABOKANKU SU KARU
Posted on: Fri, 13 Sep 2013 08:58:22 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015