ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 56 Musulmi Sun Ci Gaba Da Fuskantar Wulakanci Abdullahi bn Masud Radhiyallahu Anhu ya bayyana irin halin da musulmi suka shiga a wancan lokaci. Yana cewa: Mutane bakwai ne aka fara sanin musuluncinsu. Su ne: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da Abubakar da Ammar da mahaifiyarsa Sumayya. Sai kuma Suhaibu da Bilal ba Miqdad. Shi dai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Allah ya ba shi kariya ta hanyar baffansa Abu Talib. Abubakar shi ma da danginsa ne Allah ya yi ma sa shamaki daga gare su. Sauran kuwa sun sha azaba wadda ba ta misaltuwa. Aka rinka sanya ma su walkin karfe ana azabta su a rana. Duk cikin su babu wanda ba a dimauta hankalinsa aka tilasta shi furta kafirci ba in ban da Bilal. Shi kam babu yadda ba su yi da shi ba, har suka gaji suka mika shi ga shaidanun yara suna yawo da shi rango rango a cikin Makka. Shi kuma ba abinda yake fadi sai Ahad! Ahad!! Yana nuni zuwa ga imaninsa da tauhidi, kuma yana tabbata ma su ba gudu babu ja da baya. Musnad na Imam Ahmad, hadisi na 3832. Kuma isnadin labarin yana da kyau. Allahu Akbar! Bilal bawan Allah. Shi ba wata kabila ko wasu dangi ko wani gida da yake kariyar sa. Shi ba dan gari ba ne, ba kuma farar fata ne ba. Ba shi da karfi, ba shi da yanci domin bawa ne wanda aka saya da kudi. Amma fa yana da zuciya mai karfi, da imani mai kauri, da sadaukantaka wacce yaya masu yanci suke bukatar su koya daga wurinsa. Don haka bai fasa yin daar da ta dace ga maigidansa Umayyatu dan Khalaf ba. Amma maganar akida ya riga ya zaba ma kansa wacce yake ganin za ta fis she shi. Kuma duk wani mataki da za a dauka ba zai hana shi bayyana akidarsa ba. Ana cikin haka ne watarana Allah - cikin ikonsa - ya biyo da Abubakar Radhiyallahu Anhu ta inda Umayyatu yake azabta bawan nasa. Da Abubakar ya gane ma idonsa abin da ke faruwa sai ya tsaya ya yi ma Umayyatu waazi yana ce ma sa, ka ji tsoron Allah ka fita batun wannan taliki. Umayyatu ya kada baki ya ce, to wane ne ya lalata min shi ba kai ba? Ka saye shi kawai in kana so ka sake shi. Take sayyidina Abubakar ya karbi tayinsa; ya sayi Bilal ya yanta shi. Daga nan Bilal ya fara shakar kanshin yanci da bautar Allah a cikin sarari ba tare da tsangwama ba. Tun da yake yanzu ya zama da mai yanci kamar kowa. Shi kuma sayyidina Abubakar ba wannan ne karon farko da yake diyauta bayin Allah masu shan wahala a hannun kafirai ba. Domin shi ne ya diyauta Amir bin Fuhairata - wanda ya halarci Badar da Uhud kuma ya samu shahada a Mauna. Haka kuma ya diyauta bayi mata da dama. Cikin su har da Ummu Ubais da Zinnirah wadda kafirai suka yi ma ta duka har suka tsiyaye idonta. Kuma suka rika yi ma ta gori cewa, don tana zagin Lata da Uzza ne suka makantar da ita. Amma da ta roki Allah sai ya warkar da ita, ganinta ya dawo garau. Haka kuma Abubakar Radhiyallahu Anhu ya diyauta Nahdiyyah da yarta a lokacin da ya gan su uwargidansu ta aike su nikan gari tana fadin wallahi ba zan taba diyauta ku ba. Bayan da ya yi cinikinsu ya biya sai ya ce ma su ku ajiye ma ta garinta. Sai suka ce, ko dai mu fara kai ma ta nikan mu dawo? Ya ce, in kuna so ku kai ma ta ba laifi. As-Sirah An-Nabawiyyah na Ibn Hisham, (1/393). Akwai kuma wata kuyangar da ya isko Umar bn Khattab na azabtar da ita. Ita ma ya saye ta ya diyauta ta. Idan ana maganar wahalar da musulmi suka sha a hannun kafirai ba zai yiwu a manta da Yasir da iyalinsa ba. Asalin Yasir dan kasar Yemen ne. Alherin Allah ya ingizo shi zuwa Makka wajen neman wani dan uwansa. Ya zauna a karkashin Abu Huzaifa bn Mughirah Al-Makhzumi wanda ya aurar ma sa kuyangarsa Sumayya suka haifi Ammar. Da musulunci ya zo su duka ukun suka sa hannu biyu suka karbe shi. Makhzumawa kuwa suka rinka azabta su azaba wadda ba ta misaltuwa. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da kansa ya gane ma idonsa irin azabar da ake yi ma su. Ya rika ba su hakuri yana cewa, Ku yi hakuri iyalan Yasir, babu shakka aljanna ce makomar ku. Sahih As-Sirah An-Nabawiyyah, na Ibrahim Al-Ali, shafi na 97-98. Ita dai Sumayya Abu Jahli ne ya kashe ta. Shi kuma Yasir kaifin azaba ya gama da shi. Suka bar dansu Ammar yana dandanar zafin azaba a cikin zafin duwatsun Makka har sukan gigita shi ya furta kalmar kafirci bai sani ba don su sassafta ma sa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi ma su addua yana cewa, Ya Allah ka gafarta ma iyalan Yasir. Kuma ma ai ka riga ka gafarta ma su. Majma Az-Zawaid! Na Haithami, (9/293).
Posted on: Sat, 18 Jan 2014 21:11:43 +0000

Trending Topics




© 2015