ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Sayyadi Rasulullahi - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Sayyadi Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam 4 Kasashen Da Ke Akwai Kafin Zuwan Manzon Allah (S) 3. Qasashen Turawa Ban da wadancan kasashe da muka fada a baya akwai kasashen turawa da kuma Japan, da kasar Sin, da Indiya. Su kuma wadannan kasashen rayuwarsu ta fi kama da ta dabbobin dawa a wancan lokaci. Ba abin da ba sa bauta ma, tun daga rana da wata da ruwa da taurari har su shanu da makamantansu. Kai, har Farji ma akwai masu bauta a cikin su. Wai, saboda shi ne mafitar kowa, don haka shi ne Allan! Babu kasuwar da ke ci a cikin su sai ta almara da tatsuniya. Kuma dukkan su sun yi imani cewa, ba a tashin kiyama. Amma sun yi amanna cewa, duk wanda ya mutu zai sake dawowa duniya a wata sifa daban ba ta mutum ba. Yaallah ko kare ko biri ko mage ko wani abu daban. 4. Sai kuma Yahudawa wadanda suka yi kaka-gida musamman a kasar Sham (Syria) da Iraqi da kuma Hijaz (yankin da Saudia take ciki a yau). Su ma dai kamar Nasara sun dade da canja addininsu. Kuma sun musanya littafin da Allah ya saukar ma Annabi Musa (AS) da wasu surori da suka kago suna karantawa, inda suka mayar da Allah a matsayin ubangijinsu su kaxai ba da sauran mutane ba. Suna da wani littafi da suka kira Talmud wanda suka fifita shi a kan At- Taurah. A cikin sa sun zava ma kansu irin rayuwar da suke ganin ta dace da su a matsayin zababbun bayi wadanda Allah ya yi kowa don ya bauta masu. Haka kuma sun kitsa labarai iri daban daban na cin mutuncin annabawa da manzannin da Allah ya aiko ma su. Saannan sun yi fice wajen cin rashawa da algussu wajen sanaa da kuma kudi da ruwa. Zamu ci gaba in Allah ya so. Zamu daina amfani da (Q,V,X) wadanda mun sa su ne don masu amfani da font na Rabiat Muhammad wanda yake ba da haruffan Hausa masu lankwasa. Ku dakace mu.
Posted on: Wed, 13 Nov 2013 18:18:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015