ASHE BAKU TABA JI DAGA MANZON ALLAH (S) CEWA; 1- Duk wanda na - TopicsExpress



          

ASHE BAKU TABA JI DAGA MANZON ALLAH (S) CEWA; 1- Duk wanda na zama Maulansa to Ali ma Maulansa ne. 2- Aliyu a wajena kamar Haruna a wajen Musa ne. 3- Ali daga Ni yake, Nima daga Shi Nake. 4- Ali a wajena kamar Zuciyata ne. Binsa bina ne, Saba masa saba mini ne. 5- Yakan Ali Yakan Allah ne, kuma Amincin Ali Amincin Allah ne. 6- Masoyin Ali masoyin Allah ne, Makiyin Ali Makiyin Allah ne. 7- Ali Hujjar Allah ne akan Bayinsa. 8- Son Ali Imani ne, kinsa Kafirci ne. 9- Rundunar Ali rundunar Allah ne, kuma Rundunar Makiya Ali rundunar Shaidan ne. 10- Ali na tare da Gaskiya, kuma Gaskiya na tare da Ali, ba zasu taba rabewa da juna ba. 11- Ali ne mai rabon wuta da Aljanna. 12- Shiar Ali (Masoya da Mabiya ga Ali) sune masu rabauta ranar al- Kiyama. _______________ ___ Wannan duk Jabir bin Abdullahil Ansari ne ke bada shedar yaji da Kunnensa Annabi Muhammad (S) ya fadi wadannan Hadisan akan Falalar Imam Ali (AS). Duba Yunabiul-Muwad da na Sheik Sulaiman al-Kunduzi, al-Hanafi, As- Sunni. J-1, shafi na 172. Babi na 7. Hadisi na 22 a Babin.
Posted on: Sun, 27 Oct 2013 19:46:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015