Akwai wani saurayi dan ganye wato (wi-wi), kuma yanada gida a kusa - TopicsExpress



          

Akwai wani saurayi dan ganye wato (wi-wi), kuma yanada gida a kusa da Makabarta.. Al adanshi shine... Kullum sai yahau achaba yace akaishi makabarta, dazaran ya iso wajen sai yace da Dan achaba 'bari inshiga gida inkarbo maka kudin ka' sai kawai kaga ya shige cikin Makabarta. Dan achaba kuwa dayaga haka sai kaga ya ruga yabar wajen, sai yayita dariyan sannan ya fito ya shige gida... Akwana atashi, sai watarana yasamu wani Dan acaba mai Uban nacin tsiya... Loka cinda ya kawoshi Kofan Makabarta sai yace dashi 'Bari inshiga gida in dauko maka kudin ka', sai Dan achaba yace dashi 'yauwa bari nima inbika dan zan sha ruwa'... Hmm abin mamaki Haka suka shige cikin Makabarta da daddare... Da wannan saurayi yaga yadda wannan Dan acaban ya nace mishi saiya shawarta wata dabara acikin ranshi ta yadda zai razana wannan dan Achaban kozai rabu dashi... Ai sai gogan Naku ya wuce kaitsaye zuwa wajen wani kabari yatsuguna a bakin Kabarin sannan yasa Hannu yadan kwan-kwasa kabarin yana cewa ' Dan liti!? Dan liti! bani naira dari insallami wannan Dan Achaban!'.. Kwatsam cikin rashin tsammani saiga wani Hannu yafito PUT! Daga cikin kabarin sannan ana fadin 'Gashinan Kuma ka kawo min canji cikin sauri, dan niam inada Buka tanka!' hehehehehehe... Aida jihaka sai dukkansu suka Zabura aguje kowa ya kama Gabanshi... Bissalam..
Posted on: Sat, 21 Sep 2013 21:33:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015