An Nada Sabbin Kwamishinonin Yan Sanda 21 Mukaddashin Sufeto - TopicsExpress



          

An Nada Sabbin Kwamishinonin Yan Sanda 21 Mukaddashin Sufeto Janar na yan sandan Nigeria, Suleiman Abba, ya nada sabbin kwamishinoni a jihohi 21. =============================== Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin yan sanda Emmanuel Ojukwu ya fitar a Jiya Litinin a Abuja. Sabbin kwamishinonin da jihohinsu dai sune Usman Yakubu ( Nasarawa); Isaac Gabriel Achong (Akwa Ibom); Paul Okafor (Kogi); Hyancith Dagala (Benue); Idris Faruk Umar (Jigawa); Salihu Garba (Kwara); A. K. Shodipo (Oyo); Abubakar Marafa (Osun); Clement Adoda (Borno); and Kayode Aderanti (Lagos). Sauran sun hada da– Usman Baba (Delta); Dan Bature (Rivers); Karma Hosea Hassan (Anambra); Titilayo Busari (Cross River); Valentine Ntomchukwu (Bayelsa); Frederick Lakanu (Ekiti); Ademola Omole (Taraba); Olusola Emmanuel Amore (Niger); Adejoh Gabriel Adaji (Adamawa); Ishaku Barau (Kebbi); da kuma Wilson Inalegwu (Babban Birnin Tarayya Abuja).
Posted on: Tue, 09 Sep 2014 05:06:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015