An tambayi HASSANUL BASARI akan sirrin gujewar abin duniya da yake - TopicsExpress



          

An tambayi HASSANUL BASARI akan sirrin gujewar abin duniya da yake yi? Sai ya ce: Abubuwa ne guda hudu: - Lokacin da na san lalle Arziqi na ba mai daukan sa, sai na samu nitsuwa a zuciya ta. - Lokacin da na san cewa lalle aiki na ba mai yi mini shi, sai na shagala da shi. - Lokacin da na san cewa lalle Allah yana gani na, sai nake jin kunyar ya gan ni ina aikata sabo. - Lokacin da na san cewa lalle mutuwa tana jira na, sai shirya guzurin haduwa da Ubangijin Talikai.
Posted on: Tue, 10 Sep 2013 16:31:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015