Assalamu alaikum. Lallai malam ina tare da kai a mafi yawancin - TopicsExpress



          

Assalamu alaikum. Lallai malam ina tare da kai a mafi yawancin post da kake yi, kuma amfanuwar da nake ta fi misaltuwa. Wannan dalili ya sa naga ya kamata na isar da godia ta gareka a bayyane Allah ya saka da mafificin alkhairinsa ya sa Aljanna ta zama makoma a gareka, ya albarkaci zuriyarka, ya jikan mahaifanka, ya sa ka sami wannan hidima da kakeyi a bisa mizanin kyawawan ayyukanka. Daga dan uwanka a Musulunci SHEHU KOSHE SHIRA ZAUREN FIQHU: *************** Malam Shehu nagode. Allah ya saka muku da alkhairi. Da kai da dukkan jamaar wannan zauren. Masu yi min addua kullum. Bayan adduar da kuke yimin acikin comments, da wacce kuke turo min ta email ko BBM ko WHATSAPP, na tabbata kuna yimin ma akebance. Wannan ba karamin abu bane domin kuwa alama ce ta QAUNAR JUNA DOMIN ALLAH (swt). Kuma Allah yayi mana alkawari (ta harshen Manzonsa saww) cewar duk masu yiwa juna irin wannan kaunar, zai sanyasu acikin Inuwar alarshinsa. Sannan kuma Hadisi ya tabbatar mana cewar. Adduar Dan uwa musulmi wacce yayiwa Dan uwansa musulmi abayan idonsa, karbabbiya ce. Kuma duk abinda kuke roka min, akwai Malaika atare daku yana yi muku bisharar cewar KU MA KUNA DA KWATANKWACIN HAKA.. Don haka ina Qara godiya agareku. Kuma kullum kuna cikin adduata. Allah ya saka muku da mafificin alkhairi. Nagode. Ina so ka turo min Lambar wayarka ta email. Duk lokacin da zanje Azare zan tsaya a Shiran domin mu gaisa face 2 face.
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 12:46:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015