Barkanmu da rana. A shirinmu na karfe uku a agogon Najeriya da - TopicsExpress



          

Barkanmu da rana. A shirinmu na karfe uku a agogon Najeriya da Nijar, za ku ji cewa a arewacin jamhuriyar Nijar yanzu haka matsalar gurbatar yanayi ce ke damun mazauna yankin sakamakon yakin da aka sha gwabzawa da kuma yawaitar kamfanonin da ke hakar Uranium masu sakin iska mai kunshe da guba. A Najeriya, asusun ajiyar kundin da ake yin tsimi na kasar, wato Sovereign Wealth Fund a turance, a karon farko ya zuba dala miliyan 200 a kasuwannin hada-hadar kudi a matsayin jari. A kasar Kenya an soma makokin kwanaki uku domin alhinin rashin mutanen da harin masu kaifin kishin Islama ya rutsa da su a cibiyar kasuwanci ta WestGate da ke birnin Nairobi. Sulaiman Ibrahim Katsina ne zai gabatar da shirin. Isa Sanusi zai karanto labaran duniya.
Posted on: Wed, 25 Sep 2013 13:15:11 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015