DAGA CIKIN ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MAKA WAJAN HAKURIN NISANTAR - TopicsExpress



          

DAGA CIKIN ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MAKA WAJAN HAKURIN NISANTAR SON ZUCIYA DA DAGEWA WAJAN DAA`A: 1- KA RIKA TUNA CEWA: Mutum fa ba a halicce shi don bin abin da ransa yake so ba, Sai dai an tanadeshi ne don ya rika hangen karshensa da abin da zai biyo bayan rayuwarsa ta duniya. 2- Ka rika tunanin makomar bin abinda rai yake so, nawa-nawa ya zubar da mutuncin mai mutunci!! nawa-nawa ya jefa mutum cikin kaskanci da kunyata!!! 3- Kafin ka aikata wani abu da rankaya yi sha`awarsa na sabo, to auna a ranka kamar gashi ka yi sabon ka gama dadin da ka ji na sabon ya wuce. Sannan sai ka tuna abin da zaibiyo bayan wannan na nauyin zunubin da zai barka da shi, ga kuma kaskanci da nisantar mahaliccinka. 4- Ka auna wannan sabon da kake son aikatawa a kan wani wanda ba kai ba, idan ka ga wani mutum mai mutunci yana aikata irin wannan sabon da wacce irin kama za ka ganshi?! to sai ka tuna kai ma fa haka mutane za su rika ganinka! 5- Ka yi tunani da hankalin da Allah ya baka, lallai za ka gano cewa wannan abin da kake son aikatawa ba wani abu ne mai kima ba, kawai dai zuciyarka ce ta makance kake ganinsa kamar wani abin kirki. 6- Ka yi tunani game da izza da daukaka da wanda ya ki bin son zuciyarsa zai samu tun a nan duniya na daga kwarjini a idon jama`a da kyakykyawan yabo da sheda, da nutsuwar rai, da jin dadin rayuwar duniya cikin kwanciyar hankali, da smun lafiyar jiki....... ds. Sannan ka yi tunanin kishiyar haka da za ta sameka sakamakon bin son zuciyarka, na daga mummunar sheda da zubar da mutunci da yiwuwar kamuwa da cuta ta zahiri ko ta boye, da tashin hankali, da nesantar Allah, da nesantar mutanankirki....ds.
Posted on: Fri, 16 Aug 2013 05:58:54 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015