DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA - TopicsExpress



          

DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI Wallafar: Shaikh Prof. Umar Muhammad Labdo *** Darasi Na (19) *** =========================== DANGANTAKA DA SEREKUTA TSAKANIN SAHABBAI DA AHALUL BAITI (2) KABILAR QURAISHAWA (2)! Cigaban darasin baya: An kira Quraishawa da sunan ubansu na farko, watau Nadir dan Kinana wanda ake wa lakabi da Quraishu. Malaman nasaba suna kasa wannan Kabila zuwa gidaje goma sha biyu (12): 1. GIDAN HASHIM (BANU HASHIM): Hashim shi ne kakan Annabi(SAW) na biyu. Ya bar garinsu Makka ya tafi Yathriba (Madina) inda ya auri wata mace mai suna Sulma daga Banun Najjar, daya daga gidajen kabilar Khazraj mazaunan Madina. Sulma ta haifa masa da, Shaiba, wanda aka yiwa lakabi da Abdulmuddalib. Wannan shi ne kakan Annabi(SAW) na farko, watau uban mahaifinsa Abdullahi. Kuma ta kansa nasabar Annabi ta hadu da mutanen Madina kawunnansa. Banu Hashim su ne dangin Annabi makusanta kuma su ne ainihin Ahalul Baiti. 2. BANUL MUDDALIB. Muddalib da Hashim ‘yan uwan juna ne, ubansu daya, shi ne Abdu Munaf (sunansa na yanka Mugira). Lokacin da Hashim ya rasu, Muddalib, wanda shi ne babba, ya dauko dan kaninsa, Shaiba, daga wajen dangin uwarsa a Madina ya raine shi. Yayin da ya shiga da shi garin Makka, alhalin yana matashi, sai mutanen Makka suka zaci bawa ne ya sayo, sai suka rika kiransa Abdulmuddalib. Zuri’ar gidan Muddalib su suka fi kowa kusanci da Banu Hashim don haka su ma ake lasafta su cikin Ahalul Baiti. 3. BANU ABDIS SHAMS (KO KUMA BANU UMAYYA). Abdus Shams ma dan Abdu Munaf ne (shi da Hashim tagwaye ne), kuma shi ne uban Umayya, kakan Umawiyyawa wanda gidan ya fi shahara da sunansa. Wannan gida yana da yawan dangi kuma suna da daukaka kwarai a cikin Quraishawa. Wanda ya fi shahara a gidan shi ne Usman binu Affan, khalifar Annabi na uku kuma surukinsa mijin diyansa biyu, Rukayya da Ummu Kulthum. Sai Mu’awiya binu Abi Sufyan, Sarkin Musulmi kuma kakan khalifofin Banu Umayya, da Abul Aas binu Rabi, wanda shi ma surukin Annabi ne mijin babbar diyarsa, Zainab. Manzo(SAW) ya auri diyar wannan gida ita ce Ummu Habiba diyar Abu Sufyana, ‘yar uwar Mu’awiya. Zuri’ar wannan gida su suka fi kowa yawan ma’aikata ga Annabi(SAW), watau gwamnoni da hakimai da ya nada a garuruwa da nahiyoyi dabam-daban. 4. BANU ABDUDDARI. Abduddari da Abdu Munaf ubansu daya, shi ne Qusayyu binu Kilab. Daga cikinsu mashahurin sahabin nan ya fito, watau Mus’ab binu Umair, wanda ya tafi Madina ya share fage kafin Annabi(SAW) ya yi hijira zuwa can. Banu Abduddari su ne masu rike da makullan Ka’aba. 5. BANU ASAD. Shi Asad jikan Qusayyu ne daga dansa Abduluzza. Daga cikinsu Zubairu binul Awwam ya fito, daya daga Sahabbai goma da Annabi(SAW) ya yi musu albishir da Aljanna. Mahaifiyarsa ita ce Safiyya diyar Abdulmuddalib, kakan Manzon Allah(SAW). Watau uwarsa goggon Annabi ce ke nan. Har yau kuma, daga Banu Asad ne Khadijah(RA) ta fito, Innar Muminai matar Annabi(SAW) ta farko kuma uwar diyarsa Fadima. A nan muna iya yin tambaya: Ya Zubairu yake da Fadima? Kuma ya mijinta, Ali, wanda shi ma Safiyya goggonsa ce, yake da Zubairu? Mai karatu zai tuna Zubairu binul Awwam(RA) na cikin Sahabban da ‘yan Shi’a suke zagi, suna la’anta, suna daukan sa a matsayin wanda ya yi ridda wai saboda ya goyi bayan Innar Muminai A’isha a kan Ali a yakin Jamal. 6. BANU ZUHURA. Shi Zuhura dan uwan Qusayyu ne ubansu daya. Daga zuri’arsa mahaifiyar Manzon Allah(SAW) ta fito, watau Amina diyar Wahab dan Abdu Munaf dan Zuhura. Haka nan, manyan Sahabban nan, Abdurrahman binu Auf da Sa’ad binu Abi Waqqas, wadanda Rafilawa suke zagi suna kafirtawa, su ma daga wannan gidan suka fito. Don haka su kawunnan Annabi ne. A nan sai mu tambayi ‘yan Shi’a, wadanda suka yi batan bakatantan, don me kuke zagin kawunnan Annabi(SAW) alhali kuna da’awar kaunar mutanen gidansa? Insha Allah, a darasi na gaba za mu ji cigaba.
Posted on: Sun, 19 Jan 2014 20:36:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015