GA SHARHIN JARIDUN #NIGERIA NA WANNAN MAKO - TopicsExpress



          

GA SHARHIN JARIDUN #NIGERIA NA WANNAN MAKO (20-10-2014) #Adamu_Dan_America ke muku fatan Alkhairi da kasancewa cikin koshin Lafiya. 1. TREEBUNNE A yaune hukumar lafiya ta duniya (W.H.O) zata bayyana kasar NIGERIA a matsayin wadda bata dauke da cutar EBOLA bayan share kwanaki 42 wani bai kamu ba 2. THE PUNCH Wasu yan bindiga sunkai hari wani kauye kusada WUKARI a jahar TARABA inda suka hallaka mutane 25 yayinda sukayi gaba da dimbin dukiya 3. VANGUARD Gwamnatin tarayya tace tanada kwarin guiwar cewa yan BOKO HARAM zasu sako yan matan CHIBOK da suka sace fiyeda watanni 6 nan gaba kadan a tattaunawar da sukeyi 4. LEADERSHIP Bayan sanarwar da gwamnati tayi cewa an tsagaita bude wuta da yan B.H kwana 1 rak a tsakani sai gashi an sake kai wasu hare hare a Jihohin BORNO & ADAMAWA 5. RARIYANEWS Watanni 6 kenan da sace yan matan CHIBOK kowane hali suke ciki, suna nan lafiya ko sun mutu ko a cikin wace kasa suke, har yanzu dai iyayen yaran basu hakura ba 6. DAILY TRUST Wasu ministoci 7 sunyi murabus saboda umurnin da JONATHAN ya basu cewa kafin ranar 20/10/2014 duk mai son tsayawa takara toya ajiye mukaminsa ya koma Jiharsa
Posted on: Mon, 20 Oct 2014 10:27:32 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015