GYARA KAYANKA KASHI NA (2) RASHIN WADATAR ZUCI: Wani marubuci - TopicsExpress



          

GYARA KAYANKA KASHI NA (2) RASHIN WADATAR ZUCI: Wani marubuci yana cewa: tundaga ranar da mutum ya wannan duniyar bukatu iri-iri daban-daban suka yi masa kawanya. Kamar su tufafi da muhalli larura ce ga cigaban Dan Adam wasu bakatun kuwa ba larura ba ne, daiman suna sauyawa kuma baa taba biyansu duka. Saboda haka matukar rashin wadatar zuci ta kutso kai cikin gida musamman ta dira a kan matar gida to kullum ba za ta wadatu da abida mai gida ya kawo ba, musamman a cikin irin halin da azzaluman Shuwagabanni suka jefa kasar nan a ciki. To idan hakan ta faru babu abinda zai biyo baya sai rainuwa, shi mijin ya na ganin cewa yana iya bakin kokarinsa ita kuma tana raina masa, saboda haka sai sabani da matsaloli su yi ta faruwa. Kwadayi yana daga cikin manyan abubuwan da suke haifar da rashin wadatar zuci. Imam Ali (AS) yana cewa: Ku kiyayi kwadayi domin maabocinsa jingina ne ga kaskanci da wahala. (Gurarul hikam shafi na 135) harwalayau ya kara cewa: Kwadayi yana kashe zuciya, yana bata addini kuma yana balbaltar da kuruciya. (Gurarul hikam 77). ZAN CIGABA INSHAALLAHU!
Posted on: Wed, 30 Oct 2013 06:38:53 +0000

Trending Topics



asamune GH297 30cm 112g short for
Que Linda Boutique/Body N Soul Studio with our facilitators

Recently Viewed Topics




© 2015