HADISAI HAMSIN (50) KAN KHALIFANCIN KHALIFOFIN MANZON ALLAH (S A - TopicsExpress



          

HADISAI HAMSIN (50) KAN KHALIFANCIN KHALIFOFIN MANZON ALLAH (S A W) DA FALALOLINSU ( 8 ) HADISI (4): DAKE ALBISHIR KAN SAMUWAR KHALIFOFI (12) ; WADANDA A ZAMANINSU MUSULUNCI ZAI ZAMO MAI KARFI; MAI IZZA, DA KARIYA: … (ci gaba) NA UKU: MUHIMMAN LAMMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN USMAN (RA) WADDA SUKE NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA: Gabanin ambato muhimman abubuwan da suka auku a khalifancin zun-nuwraini Usmanu bn Affana (RA) wadanda su ke nuna cewa musulunci bai gushe ba yana da izzah a wadancan shekarun (23-35) dama wadanda suka gabace su dana bayansu: zai yi kyau mu nazarci hadisi ingantacce da Imamul Bukhariy (RL) ya ambace shi muallaq a wuri biyu, da ke nuna cewa a zamanin manzon Allah (SAW) sayyiduna Usman na cikin jigajigan masu dukiya, da su ka yi amfani da ita wajen ciyar da addinin Allah gaba. Ga lafazin hadisin a wuri na biyu [gabanin hadisi mai lamba: 3695] : قال النبي : «مَنْ يَحْفِرْ بِئْرَ رُومَةَ فَلَهُ الْجَنَّةُ» فَحَفَرَهَا عُثْمَانُ. وقال: «مَنْ جَهَّزَ جَيْشَ الْعُسْرَةِ فَلَهُ الْجَنَّةُ» فَجَهَّزَهُ عُثْمَان. Maana: (Annabi –SAW- ya ce: Wanene zai tona rijiyar ruwmah, ko ya saye ta; sakamakonsa aljannah? Sai Usman ya tone ta. Ya sake cewa: Wanene zai shirya rundunar da za ta tafi yakin tabuka, sakamakonsa aljannah? Sai Usman ya shirya rundunar. Wadannan maganganun guda biyu Imamul Bukhariy ya ambace su ne bayan fadinsa: باب مَنَاقِب عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ . Gabanin haka kuma ya riga ya ambace su da isnadi muallaq zuwa ga Abu-abdirrahman ya ce: (أَنَّ عُثْمَانَ حَيْثُ حُوصِرَ أَشْرَفَ عَلَيْهِمْ، وَقَالَ: أَنْشُدُكُمْ -وَلاَ أَنْشُدُ إِلاَّ أَصْحَابَ النَّبِيِّ - أَلَسْتُمْ تَعْلَمُونَ أَنَّ رَسُولَ اللهِ قَالَ: مَنْ حَفَرَ رُومَةَ فَلَهُ الْجَنَّةُ فَحَفَرْتُهَا؟ أَلَسْتُمْ تَعْلَمُونَ أَنَّهُ قَالَ: مَنْ جَهَّزَ جَيْشَ الْعُسْرَةِ فَلَهُ الْجَنَّةُ فَجَهَّزْتُهُمْ، قَالَ فَصَدَّقُوهُ بِمَا قَال). Maana: (Lallai Usman -RA- a lokacin da wawayen mutanen da su ka je Madina daga Masar da waninsa suka killace shi gabanin kashe shi ya leko ya ke cewa: Ina hada ku da Allah –ba ga kowa na ke wannan magiyar ba sai ga sahabban da su ka rayu da annabi SAW-: Shin ba ku da sanin cewa lallai manzon Allah -SAW- ya ce: Wanene zai tona rijiyar ruwmah ko ya saye ta; in ya yi haka sakamakonsa aljannah. Sai na tone ta? Shin baku da masaniyar cewa, -Annabi SAW- ya ce: Wanene zai shirya rundunar da za ta tafi yakin tabuka, sakamakonsa aljannah, Sai na shirya rundunar? Sai su ka gaskata shi kan abin da ya fada). [Sahihul Bukhariy, lamba: 2778]. Dangane da abin da Usman ya yi na shirya mayakan da suka tafi yakin tabuka, Karin bayani ya zo a cikin [Jamii na At-tirmiziy, lamba: 3701 Albaniy kuma ya ce: hadisi ne hasan a cikin mishkaatul masabih, lamba: 6073]: عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ سَمُرَةَ، قَالَ: جَاءَ عُثْمَانُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِأَلْفِ دِينَارٍ، فِي كُمِّهِ، حِينَ جَهَّزَ جَيْشَ الْعُسْرَةِ فَنَثَرَهَا فِي حِجْرِهِ. قَالَ عَبْدُ الرَّحْمَنِ: فَرَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَلِّبُهَا فِي حِجْرِهِ وَيَقُولُ: مَا ضَرَّ عُثْمَانَ مَا عَمِلَ بَعْدَ اليَوْمِ! مَرَّتَيْنِ. Maana: (Abdur-rahman bn Samurah ya ce: Usman ya zo zuwa ga annabi –SAW- da dinari 1000, a cikin hannun rigarsa, a lokacin da ya shirya mayakan tabuka, sai ya zuba su a kirjinsa. Abdur-rahman ya ce: Sai naga annabi –SAW- yana ta jujjuya su a kirjinsa yana cewa: Abun da Usman ya aikata bayan wannan yini ba zai cutar das hi ba. Sau biyu). Kuma yana daga cikin abin da Usman ya aikata ga daukacin musulman zamanin manzon Allah (SAW) da wadanda su ka zo bayansu, sayan fili da ya yi, wadda annabi (SAW) ya kara masallacinsa da shi, A cikin hadisin Sumamah bn Alhazan mai tsayi; wadda yawancin jumlolinsa sun tabbata cikin hadisai ingantattu, kamar yadda ambatonsu ke tafe, haka kuma Imam At-tirmiziy yace: hadisi ne hasan [lamba: 3703]ya zo cewa: عَنْ ثُمَامَةَ بْنِ حَزْنٍ القُشَيْرِيِّ، قَالَ: شَهِدْتُ الدَّارَ حِينَ أَشْرَفَ عَلَيْهِمْ عُثْمَانُ، فَقَالَ: ائْتُونِي بِصَاحِبَيْكُمُ اللَّذَيْنِ أَلَّبَاكُمْ عَلَيَّ. قَالَ: فَجِيءَ بِهِمَا فَكَأَنَّهُمَا جَمَلانِ أَوْ كَأَنَّهُمَا حِمَارَانِ، قَالَ: فَأَشْرَفَ عَلَيْهِمْ عُثْمَانُ، فَقَالَ: أَنْشُدُكُمْ بِاللَّهِ وَالإِسْلامِ هَلْ تَعْلَمُونَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَدِمَ المَدِينَةَ وَلَيْسَ بِهَا مَاءٌ يُسْتَعْذَبُ غَيْرَ بِئْرِ رُومَةَ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ يَشْتَرِي بِئْرَ رُومَةَ فَيَجْعَلَ دَلْوَهُ مَعَ دِلاءِ المُسْلِمِينَ بِخَيْرٍ لَهُ مِنْهَا فِي الْجَنَّةِ»؟ فَاشْتَرَيْتُهَا مِنْ صُلْبِ مَالِي فَأَنْتُمُ اليَوْمَ تَمْنَعُونِي أَنْ أَشْرَبَ مِنْهَا حَتَّى أَشْرَبَ مِنْ مَاءِ الْبَحْرِ. قَالُوا: اللَّهُمَّ نَعَمْ. فَقَالَ: أَنْشُدُكُمْ بِاللَّهِ وَالإِسْلامِ هَلْ تَعْلَمُونَ أَنَّ المَسْجِدَ ضَاقَ بِأَهْلِهِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ يَشْتَرِي بُقْعَةَ آلِ فُلانٍ فَيَزِيدَهَا فِي المَسْجِدِ بِخَيْرٍ لَهُ مِنْهَا فِي الجَنَّةِ»؟ فَاشْتَرَيْتُهَا مِنْ صُلْبِ مَالِي فَأَنْتُمُ اليَوْمَ تَمْنَعُونِي أَنْ أُصَلِّيَ فِيهَا رَكْعَتَيْنِ؟ قَالُوا: اللَّهُمَّ، نَعَمْ. قَالَ: أَنْشُدُكُمْ بِاللَّهِ وَبِالإِسْلامِ، هَلْ تَعْلَمُونَ أَنِّي جَهَّزْتُ جَيْشَ العُسْرَةِ مِنْ مَالِي؟ قَالُوا: اللَّهُمَّ نَعَمْ. ثُمَّ قَالَ: أَنْشُدُكُمْ بِاللَّهِ وَالإِسْلامِ هَلْ تَعْلَمُونَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ عَلَى ثَبِيرِ مَكَّةَ وَمَعَهُ أَبُو بَكْرٍ وَعُمَرُ وَأَنَا فَتَحَرَّكَ الجَبَلُ حَتَّى تَسَاقَطَتْ حِجَارَتُهُ بِالحَضِيضِ قَالَ: فَرَكَضَهُ بِرِجْلِهِ وَقَالَ: «اسْكُنْ ثَبِيرُ فَإِنَّمَا عَلَيْكَ نَبِيٌّ وَصِدِّيقٌ وَشَهِيدَانِ؟» قَالُوا: اللَّهُمَّ، نَعَمْ. قَالَ: اللَّهُ أَكْبَرُ شَهِدُوا لِي وَرَبِّ الكَعْبَةِ أَنِّي شَهِيدٌ، ثَلاثًا. Maana: (Ya zo daga Sumamah bn Hazn al-kushairy, yace: Lallai na halarci ranar da aka killace Usman a cikin gidansa, lokacin da ya leko ta Katanga yace musu: Ku zo min da mutum biyu da suka tunzuro ku a kaina, Ya ce: Sai aka zo da su, kai kace su rakuma ne guda biyu ko jakuna. Ya ce: Sai Usman ya leko ta saman Katanga, ya ce: Ina hada ku da Allah da kuma girman musulunci; Shin ba ku san cewa manzon Allah –SAW- ya zo madina alhalin babu wani ruwan da ake jin gardin shansa ba in banda rijiyar ruwmah, Sai manzon Allah –SAW- ya ce: Wanene zai sayi rijiyar ruwmah; sai ya sanya gugarsa tare da gugan musulmai, sai Allah ya masa canjin wanda ta fita alkhairi a gidan aljannah? Sai na saye ta, daga tsaban dukiyata; Amma sai ga shi a yau ku kuma kuna hana ni na sha ruwa daga gare ta, sai dai na sha ruwan teku mai zartshi! Su ka ce: haka ne wallahi! Sai ya sake cewa: Ina hada ku da Allah da kuma girman musulunci; Shin ba ku san cewa masallacin annabi –SAW- ya yi kunci da karanta ga masu sallah a cikinsa ba, Sai manzon Allah –SAW- ya ce: Wanene zai sayi filin kabilar wane, sai ya kara mana shi a masallaci, sakamakonsa shi ne filin da yafi wannan alkhairi a gidan aljannah? Sai na sayi wannan filin daga tsabar dukiyata, amma sai gashi a yau kun hana ni nayi salla rakaa biyu a cikinsa? Sai su ka ce wallahi haka ne! Ya ce: Ina hada ku da Allah da kuma girman musulunci; Shin ba ku san cewa lallai nine na shirya rundunar da ta tafi yakin tabuka, daga dukiyata ba? Sai su ka ce: e wallahi haka ne! Saannan ya ce: Ina hada ku da Allah da kuma girman musulunci; Shin ba ku san cewa lallai manzon Allah -SAW- ya kasance akan dutsen Sabiir da ke garin makka, a tare da shi akwai Abubakar da Umar da kuma ni, sai dutsen ya girgiza har kananan duwatsu da su ke kansa su ka farfado kasan babban, amma sai annabi –SAW- ya canke shi da kafarsa, sannan ya ce: Ka tabbata dutsen sabiir; saboda ba kowa ba ne akanka face annabi da Siddiqi da mutum biyu da za su yi shahada? Sai su ka ce e; haka ne wallahi! Sai ya ce: Allahu akbar!!! Sun yi min shaida cewa ni shahidi ne. Sau uku! ). Wadannan kadan ne daga cikin manya-manyan misalai da su ke nuna yadda Usman (RA) ya sadaukar da dukiyarsa, wajen taimakon musulunci da daukaka kalmarsa a zamani ko rayuwar manzon Allah (SAW); ta yadda ya kasance mutumin da ya fi dukkan musulmai ko kuma daga cikin wadanda suka fi kowa sadaukarwa da dukiyarsu, a lokacin bukatarta. Amma dangane da muhimman abubuwan da su ka auku a tsawo ko zamanin halifancin Usman (RA) da ya kai shekaru goma sha biyu (wato daga shekara 23-35 na hijira) masu nuna izzar musulunci da yaduwarsa, da kuma yadda musulmai su ke da kwar-jini a idanun makiyansu: (((Zamu ci gaba bi iznillahi taalah!)))
Posted on: Tue, 04 Mar 2014 23:55:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015