ILIMI KOGI NE.. Filin Fatawa da harkokin addini.. ****** KU - TopicsExpress



          

ILIMI KOGI NE.. Filin Fatawa da harkokin addini.. ****** KU KUKE GURBATA TARBIYYAR YAYANKU TUN KAFIN SU SHAKI ISKAN DUNIYA -Kun kangare daga yi ma Iyayenku biyayya tun kuna karkashin inuwarsu.. Sai Yayanku suma suka bijire maku. -Ka lalata yar wani, shima dan wani ya lalata taka, Inji Annabi SAW. ko kuma danka yayi gadon tsiya. -Kin kasance kangararriya,mare kamun kai, mashirkiya.... Muggan dabiunki zasu bi jijiyar jinin Yayanki. Hadisi ne daga Annabi SAW yake fada ma Aliyu R.A a lkcn da zaije neman auren diyar Abu Jahl ya hana shi zuwa da cewa Dabia tana bin jijiya. Abu Aswadud Duwali yace ma Yayansa Hakika na kyautata maku yarintarku da tsufarku tun kafin in haifeku sai yaran suka tmbyeshi dalili, yace Na zabar maku #Uwa wacce ba zaku zargeta ba -Ka gaza wajen zaba masu Uwa tagari/Kin gaza wajen zaba masu Uba Nagari wanda shine hakkin Yaya na farko akan Iyayensu. Wani Uba ya kawo karar dansa wajen Umar RA cewa baya masa biyayya, sai Umar RA ya fara ma yaron waazi, sai yaron ya tmby Umar RA cewa shin Yaya suna da hakki akan Iyayensu? yace Eh 1. Ya zabar ma dansa Uwa Tagari. 2. Ya sanya masa Suna mai kyau. 3. Ya koya masa Qurani. Sai yaron yace Ya Amirul Muminin ni bai min ko 1 daga ckn 3 ba; domin ni da ya tashi zabar min Uwa sai ya auro Karuwar maguzawar kasar Sudan, sannan bai samin suna mai kyau ba sai Gungura kashi, kuma bai taba koya min Qurani ba. sai Umar RA yace #Ashe kai ka saba ma danka tun kafin yazo Duniya ka wulakantashi. -Ka ciyar da Iyalanka da Haram, sai su taso a kangare. Annabi SAW yace Tsokar da ta tsiro ta hanyar Haramun, Wuta itace tafi dacewa da ita (Makoma). Bukhari. -Ka Zalunci Yar wani ta hanyar zamantakewar aure, kaima sai a Cutar da taka / Kin hainci dan wani ta hanyar zamantakewar aure,kema sai ai ma naki. (#Maryam_Umar).. #WAIYAZBILLAH.....! - Wani tanadi ka/kika yi ma yaranki kafin su zo duniya? - Shin kin/ka taba tunanin gyara Munanan Dabiunki/ka ko don Yayanki/ka su jonu da kyakkyawar dabia daga jijiyarki/ka? -Wace niyyace a Zuciyarka game da kalar Matar da zaka aura? Don Dukiyar mahaifinta kadai? Ko don Ita Kyakkyawa ce Zallah? Ko kuwa don Addininta da kyan hali? -Wace Niyya ce a Zuciyarki game da Mijin Aurenki? Don Yana da Kudi kawai? Ko don kyawunshi? Ko kuwa don kyawun Dabiunsa? Ko ma dai wace irin niyyace gareku ya kamata ku farka kuma ku tuna cewa Tarbiyya da hakkokin Yayanku suna daure da wuyanku tun kafin ku haifesu. Nasan kuna da abin cewa bismillah... #Mai_Gabatarwa_Mashkur
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 20:39:18 +0000

Trending Topics



ress.com/Early-morning-reflection-People-with-no-money-have-genuine-topic-10204829088476561">Early morning reflection: People with no money have genuine
A SMALL LIST OF WHITE CELEBRITY SINGLE MOTHERS JACKIE KENNEDY
There are now, officially, no good reasons to not try this
A new backpack may be one of the many items on your child’s
The bleak future of carers of the disabled: Struggling families

Recently Viewed Topics




© 2015