ISGILANCI DA RAINI Ya dan uwa musulmi ka sani raunanan mutane suna - TopicsExpress



          

ISGILANCI DA RAINI Ya dan uwa musulmi ka sani raunanan mutane suna fakewa da yin isgilanci da raini a matsayin hanyar dauke hankalin jamaj’a dagakansu, ko su yi amfani da kambama aibukan mutane wannan kuwa haramun ne, saboda ba a samun gyara ta hanyar isgili ko raini, watakila ma ya zamo hanyarkara sabo da barna, Allah Madaukakin Sarki ya ce: }يأيها الذين ءامنوا لا يسخر قوم من قوم عسى أن يكونوا خيرا منهم ولا نساء من نساء عسى أن يكن خيرا منهن ولا تلمزوا أنفسكم ولا تنابزوا بالألقب بئس الإسم الفسوق بعد الإيمان{الحجرات: 11 “Ya ku wadanda suka yi imani ka da wasu mutane suwulakanta wasu, watakila suzama mafiya alheri daga su, (masu isgilancin) kada ma mata su wulakanta mata, watakila su ma wadanda aka wulakanta din su zama mafi alheri daga wadanda suka yi isgilancin. Ka da ku yiwa kawunanku zunde kada kuma ku kira junanku da munanan lakabi, tir da sunan fasikanci bayan mutum ya yi imani”. Ma’anar Isgilanci shi ne: wulakanci da tozartawa, ko nuni ga aibun wani ko tawayarsa ta fuskar yi masa dariya, za a iya yin hakan ta hanyar Magana ko nuni ko kwaikwaya. Nana Aisha – Allah ya kara mata yarda ta ce: Na taba kwaikwayar wani mutum sai Annabi (S.A.W.) ya ce min: "والله ما أحب أني حاكيت إنسانا ولي كذا وكذا" أبو داود. “Wallahi b azan so in kwaikwayi wani mutum ba, a ba ni kaza da kaza”. Abu Dawud ya ruwaito shi. Abu Dawud ne ya ruwaito shi. Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara yarda a gare shi ya fada a game da tafsirin fadin Allah: }ووضع الكتب فترى المجرمين مشفقين مما فيه يقولون يويلنا مال هذا الكتب لايغادر صغيرة ولا كبيرة إلاأحصها{الكهف: 49 “Suna cewa me ya sami wannan littafi ne ba ya barin karami lo babban laifi face sai ya kididdige shi”. Dan Abbas ya ce: karamin laifi shi ne murmushin isgilanci ga mumini, babban laifi kyalkyala dariya a gare shi. Wannan yana nuna irin yadda yi wa mutane dariya yana daga cikin manya – mayan zunubai. Daga cikin nau’o’in isgilanci yi wa masu addinin da lazimtar hanyar Allah isgilanci, domin yi wa irin wadannan mutanen isgilanci yana nuna raunin addini da imani, hakan ma zai iya jan mutum zuwa ga ridda da fita daga musuluncigaba daya, Allah yak are mu. Imam Ibnu Taimiyya – Allah ya ji kansa – yana fada dangane da fadin Allah Madaukakin Sarki: }قل أبالله وءايته ورسوله كنتم تستهزءون * لاتعتذروا قدكفرتم بعد إيمنكم{التوبة: 65 “Ka fada cewa shin da Allah da ayoyinsa da manzonsa kuke yin isgilanci, ka da su ba da wani uzuri, hakika kun kafirta bayan kun yi imani” (Taubah: 65-66). Wannan ayar tana nuni cewa yin isgilanci da Allah da Manzonsa kafirci ne. Sheikh Iban Baz ya ce: Yin isgilanci ga musulunci ko da wani abu na musulmi kafircine tsantsa, duk wanda yak e wa ma’abota addini masu kiyaye sallah bai halata a zauna da su ba, ko a wannanaiki da suke yi, a kuma tsoratar da mutane daga gare shi, haka nan wanda yake kutsawa cikin matsalolin addini da isgilanci kafiri ne. Subhanallah.
Posted on: Sat, 24 Aug 2013 09:23:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015