Image ILIYA DA YAM FASHI Wata rana Iliya na zaune yana shan - TopicsExpress



          

Image ILIYA DA YAM FASHI Wata rana Iliya na zaune yana shan iska ya wani katon lambu a bakin kogi, yana kallon yadda kwalekwale ke ta yawo bisa ruwa, ga tsuntsaye iri iri suna kiwo, sai ya tuna da yaki. Ya tuna irin hadarin da ya shiga, da kuma wanda zai shiga. Ya ce, Allah Sarki, tsufa ne, Na tsufa, dokina ya tsufa, amma ga shi zuciyata ba ta gaza ba. Ya yi farat ya tashi ya ce, Zama wuri daya tsautsayi in ji kifi. Ya kamata mu shiga duniya mu ga abin da ta ke ciki. Da isarsa gida, sai ya jefa wa Kwalele sirdi, ya yi shiri ya kama hanya ya yi ta tafiya. Tun yana ganin alamar karkara, har ya zama ba ya ganin kome sai daji. Ya yi ta tafiya har ya tarad da wani wuri inda hanya ta kasu uku. Daya ta nufi dama, daya hagu, dayar kuwa ta mike gaba totar. A daidai wurin da hanyoyin nan suka hadu, an yi rubutu bisa wani dutse mai fadi an ce --- Wanda ya bi hanyar hannun dama, zai sami isasshiyar dukiya. Wanda ya bi hanyar hagu, zai sami mata wadda ba kamarta, Wanda ya mike totar kuwa zai gamu da mutuwarsa. Iliya ya tsaya, ya karanta ya yi shiru yana tunani, sa an nan ya ce, Ni da na ke tsoho, me zan yi da dukiya? Me kuma zan yi da mace? Bari im bi hanyar da zan gamu da mutuwar tawa in gani. Na sani dai kushewar badi sai badi. Mai rabon gain badi kuwa sai ya gani. Iliya ya sakam ma Kwalele linzami, ya zarce sosai ta tafi. Can ya shiga cikin wani surkukin daji mai duhu. Ba zato sai ga shi gaban taron yam fashi, mutum dubu hudu, da babbansu guda. Ko wanne yana rike da kayan fada iri iri. Suna jira ne kawai wani ya fado, ya bakunci lahira. Ba su ankara ba sai ga Iliya gab da su. Suka yi mamaki, don sun tabbata ba mahalukin da ke iya shiga dajin nan. Suka daka masa tsawa suka ce, Kai mai dokin nan tsaya! Iliya ya tsaya cif, har suka zo wurin da ya ke. Suka ga dokin ba irinsa duk cikin yakin kasar. Suka ce, Ina za ka? Me ya kawo ka nan wurin? Iliya yace, Na biyo hanya ne zan wuce, ban san zan gamu da ku ba. Sai babbansu yace, Ba ku gani har wani kallon hadarin kaji ya ke yi mana? Kila yana wani dan gani-gani ne gare mu ko? Iliya kuwa lalle a kaikaice ba a ya ke musu. Ya sunkuyad da kansa ya ce, Haba samari, tsofai-tsofai da ni, gani-ganin me zan muku? Ba ni da kome sai yan kudin guzuri fam dari. Wannan damarar ta zinariya da du ke gani, duka duka kudina bai fi fam dari biyar ba. Rigara kuwa tsofuwa ce, kudinsa ba zai shige fam dubu uku ba, takalmana da hulata kudinsu da kyar zai yi fam goma. Wadannan likkafun da ku ke kallo tsofuwar azurfa ce, jauharin da aka lillika musu shi ke sa ku ke ganinsu kamar wani abin kwarai, kudinsu fam dubu ne kawai. Sirdina, ko da ya ke na karfe ne, ba zai wuce fam metan ba. Dutsen nan da ke bisa kan dokina kuwa, kun dai san darajarsa. Ba shi da wani amfani, sai don ya kara wa dokin gani idan dare ya yi. Dokin kuwa ba shi da wani amfani im ba wurina ba. To, me zai sa ku tare ni? Ni ba ni da kome, ina rokonku ku kyale ni in wuce. Yam fashi su ka ce wa Iliya, Tun da mu ke tare mutane, ba mu taba samun sakarai, mahaukaci, kamarka ba. Babbansu ya ce su kama Iliya. To, a kusa da wani katon itace kuwa su ke tsaye, wanda ba kamarsa duk wurin. Da ganin jama an nan ta yunkuro za su kama shi, sai ya yi wuf ya zaro kibiya ya dubi katon icn nan ya sakam masa. Itacen nan ya ratattake ya fadi ricaa! Kamar dai tsawa ce ta fada masa. Karfin iskar faduwar itacen nan da karar fasuwarsa, ta sa yam fashin nan duk suka fadi kas somammu. Da suka farka, sai babbansu ya ce wa Iliya, Mun yarda kai ne shugabanmu. Muna rokonka, ka zauna tare da mu, ka zama babbammu. Muna da dukiya, zinari da azurfa da lu ulu u da jauhari da tufafi iri iri, ga kuma dabbobi. Duk yawammu im muka taru ko mun shekara goma ba za mu iya gama kidayar zinari da ke gare mu ba. Mun yarda ka debi duk abin da ka ke bukata, mu dai ka zama shugabanmu. Iliya ya yi dariya, ya yi wakar nasara, irin ta mayaka. Sa an nan ya ce, Yan uwana, ba ni so in wahalad da kaina don tsaron dukiya, ko kiwon dabbobi. Ni bukatata in yi yiwo cikin duniya, in yi yaki. Dukiya kuma da dabbobi, tajirai da makiyaya su tsare. Na gode muku kwarai, sai wata rana. Suka yi ban kwana, ya karya linzami ya koma da baya, ya zo wurin dutsen nan na mararraba mai rubutu. Daga gefen inda aka rubuta, Wanda ya bi hanyar da ta mike total zai hadu da mutuwarsa, sai ya rubuta: Ni Iliya-dam-mai-Karfi, na bi hanyar nan da ta mike, amma ban gamu da mutuwa ba. Daga nan ya karya linzami ya bi hanyar da ta nufi hagu, inda aka rubuta za a sami mace, ya yi ta tafita. Bayan kamar kwana biyu yana tafiya, ran nan sai ga shi ya tinkari wani irin gida mai ban mamaki. Shi dai ya fi girman gida, amma bai kai gari ba. Ginin gidan duk an yi shi be da wani irin farin karfe, sai kyalli ya ke kamar madubi. Rufin gidan kuma kansa da zinari aka yi, ga tagogi kuma na madubi, ko wacce an sa mata labule iri dabam. Akwai furanni iri iri kewaye da gidan, akwai kuma lambu cike da kayan marmari. Iliya bai tsaya ba, sai ya tasam ma kofar gidan. Tun kafin ya kai, sai ga yam mata arba in, ko wacce ta ce ado, daga kayan gwal, sai tufafin farin siliki, sai alharini, sun fito taryarsa. Suka kewaye shi suna yi masa maraba, har suka iso kofar Sarauniya. Yam mata nan su uka rike masa sirdi ya sauka. Aka fada wa Sarauniya
Posted on: Mon, 09 Sep 2013 16:13:26 +0000

Trending Topics



;">
JAKARTA FAIR - HARAJUKU COSPLAY PARTY HUT DKI - JAKARTA FAIR
Ayyaantuu News : Ogaden: ONLFs 30 Years Commemoration - By Ahmed

Recently Viewed Topics




© 2015