JAWABIN SAYYID ZAKZAKY (H) A RANAR GHADIR 1434 ___________Kashi - TopicsExpress



          

JAWABIN SAYYID ZAKZAKY (H) A RANAR GHADIR 1434 ___________Kashi Na 4 ___________ Cigaba....... .......Islam din da babu Wilayati Ali, Allah bai yarda da wannan ba. Musuluncin da Allah ya yarda da shi shi ne mai Wilayar Ali. Akace wani Bayahude yaje wajen Umaru dan Haddabi, yace masa, a cikin al-Kuraninku akwai wata aya, da mu alummar Yahudu ne aka saukar mana, da mun dauki ranan ranar Idi. Sai yace mece ce wannan ayar? Sai yace Masa AlYauma Akmaltu Lakum Dinakum....... Sai Umar yace masa to ai dama ta sauka ran Arfa ne, kuma Arfa dama Idi ne. Ya Umar! Arfa Idi ga wane? Yanzu in tambayeku, da ranar Sallah, wani abin farinciki zai sameka, ya zama ranar sallah, kuma ranar Sallan ma mu kaddara Sallar Layya, ran nan kuma ran nan ne ake rada sunan Danka, ran nan zaai ma Danka suna. An haifa maka yaro ya zama ranar sunansa ranar Layya ne. To rannan ba ruwanka da Suna layya zakayi kawai? Ko kuwa zaka hada da suna Kuma? Ina tambaya ne, in ka yanka ragon layya shikenan? Koko zaka yanka na suna kuma? Yauwa, kaga kana murna biyu kenan. Kaga yanzu rannan ya zama ranar Biki. To koda ranar Arfa aka saukar da wannan ayar, ai dole a zauna ai bikin saukan wannan ayar. Domin Arfa, wake bikin Arfa? Wanda sukaje Hajji sukan tattaru a waje guda. Amma Sauran Mutane fa? Idi ne garesu? Ina tambaya ne, ranar Arfa ranar Idi ne ga sauran Mutane? Hattama Mutanen Arfa gaskiya ba Idi ne garesu ba. Tunda meye maanar Idi, ba kana Murna bane? To ku gaya min, in kaje hajji ran nan ne ranar shan wahalar Mahajjata. Tun ba ma a tafiyan da ba. Ran da Allah (T) yake cewa; Wal-Yakdu Tafakahum..... Maana su kawar da kazantansu dan mutum yakan taso daga Arfa biji biji ne. Tin ba tafiyan da ba. Butu butu da kura. Da ihiramin nan yayi Dauda. Dan haka shi rannan ba ranar murna bane a wajenshi. Idi yana nufin ranar Murna ne. Toh naam. Ba ranar Arfa aka saukar da Al Yaumu akmaltu lakum Dinikum ba. Ranar 18 ga wata ne. Kuma rannan ranar Idi ce. A takaice, a babin tunatarwa, sai muce; bayan duk abubuwa na addini sun sauka sun kusa kammala, wannan wilayar shi kawai ya rage, sai Hajji. Hajji da Wulaya su kawai suka rage. Annabi (S) bai nuna ma mutane yadda ake yin Hajji ba. Dama akwai hajji tun zamanin Annabi Ibraheem (AS). Akwai Hajjin Annabi Ibrahim (AS). Wanda shi ne Allah (T) ya umurceshi yai kira izuwa ga Hajji. Wa Azzin fin Nasi bil Hajji, Yaatuka Rijalan Waala kulli damirin yaatuka min kulli fajjin amik Annabi Ibrahim ne aka umurceshi da yai kiran Hajji, kamar yadda ake kiran Sallah. Ake wazana. Ace Hayya alal Salah, Hayya alal Falah Haka Annabi Ibraheem yayi kiran Hajji. Tun daga nan ake Labbaikal Lahumma Labbaik. Ake amsawa ana tudada zuwa hajji. Da lokaci yayi nisa, aka ki bin Umurnin Ausiya, dan akwai Ausiya na Ibraheem. Wanda nace muku Abudalib (AS) shine karshen Ausiya. Toh aka ki bin Umurnin Ausiya aka canza Hajji, aka mai she shi bautan gumaka. Suka kakkawowadansu abubuwa a addini. Suna zuwa Arfa, amma wai su mutanen Quraish sai su tsaya a Musdalifa wai su basa karisawa Arfa wai su Manya ne. Sannan kuma akanyi Dawafi, amma sukance wai ba zakayi Dawafi da rigar da ka sabawa Allah ba. Saboda haka sai kazo ka ari rika wajen Baquraishe sai kai Dawafi. In baka da riga baka sami bakuraishen da ya baka aron riga ba sai kayi tsirara. Maza suyi da rana, mata suyi da Daddare. Suka sassaka gumaka a gefen Kaaba, suka maishe shi wasu aladu da ya fandare daga tafarki. Saboda haka yanzu wannan Manzo yazo ya nuna musu Hajji Sahihi, Hajjin Ibraheem (AS). Saboda haka sai yayi hajji ya nuna ma mutane ga yadda ake Hajji. Dama ya bude Makka yarusa gumaka. An kawar da gumaka. Hajjin farko bayan bude Makkah, wanda akayi tare da Mushirikai a shekara ta 8 bayan hijira, ainihin akai Hajji tare da kowa da kowa, Mushrikai sukai nasu, Musulmai sukai nasu. Shekara ta 8 shine aka bude Makkah, a wannan shekarar Mushirikai sunyi Hajjinsu irin na Mushrikai, Muminai ma sunyi Hajjinsu irin na Muminai. A shekara ta 9 bayan Hijira, Manzon Allah (S) ya turo Ali (AS) da Suratul Baraa. Ya karanta musu. An gama. Daga yanzun an ba Mushirikai waadin wata hudu, ko su Musulunta ko su bar gari, amma baa yarda su sake zaunawa a wannan garin suyi irin Hajjinsu ba. Shekara ta karshe, ta 10 bayan Hijira, Shine Manzon Allah (S) yazo yai Hajji da kansa. Shekara ta 11 bayan Hijira a watan Safar Allah ya karbeshi izuwa ga Rahamarsa. Saboda haka sai aka umurci Manzon Allah da yayi Hajji, dan ya nuna ma Mutane Hajji. Kuma ak nuna masa addini ya kammala saura abu biyu; da Hajji da Wilaya. Hajji cikin shika shikan Musulunci, Wilaya cikin Shika shikan Imani. Dazu ina gaya muku shika shikan Imani guda biyar, to akwai kuma shika shikan Musulunci shi ma guda biyar. Sallah, Azumi, Zakka, Hajji, da kuma Jihadi (Amru bil Maaruf wa Nahayu anil Munkar), shine na biyar. Amma qayannan shika shikan Imani, wayannan shika shikan Musulunci, wayannan Aqida, imani a zuciya, wadannan kuma aiki da gaba. Saboda haka sauran abubuwa an nuna musu na shika shikan addini. An nuna musu kaidojin Sallah, an numa musu Azumi da Zakka da Jihadi. Duk an koya musu. Yanzu abin da ya rage baa koya musu ba shine Hajji. saboda haka kunga 1 a shika shikan Musulunci, daya a shika shikan Imani. Akace masa saura wadannan. Saboda haka Manzon Allah (S) yasa akai yekuwa, duk wanda yake da halin Hajji, wanda duk yai Imani da Lailaha Illallah Muhammadur Rasulullah. In yana da halin hajji. To baa dauke masa ba. Wannan yekuwa yaje duk duniyar Musulmi na wancan lokacin. Kuma zamanin Annabi (S) Musulunci ya bugi Sham yaje su Bahrain ya buga Yemen yai Misra, yaje wurare da daman gaske na duniya. Saboda haka duk wadannan sassa duk an sanar da su; duk wanda yake da hali baa dauke masa Hajji ba. Saboda haka, mutane kowa, duk mai hali, ya shirya ya kama hanyar Hajji. Shima Manzon Allah (S) lokacin ya tura Ali (AS) Yaman, Kasar Yemen da nufin daawa. Saboda haka sai ya aika masa ya same shi. Shima ya wuce, daga nan Yemen ya wuce Hajji. Sannan Manzon Allah (S) ya tashi da Iyalan gidansa, da duk wanda zasu iya Hajji daga cikin Sahabbansa. Cikin wanda sukaje Hajjin kuma, Har da Abubakar da Umar da Usman. Cikin Matansa kuma har Aishatu da Hafsatu. Da kuam Yarsa Sayyada Fatimatuz Zahra (SA), duk suka nufi Hajji. INSHA ALLAH GOBE ZANCI GANA. AI MIN AFUWADA DAN ABIN DA YA SAMU YAU.
Posted on: Mon, 28 Oct 2013 23:13:23 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015