KASADA! Kwance nake ina ta juye - juye da zummar barci barawo - TopicsExpress



          

KASADA! Kwance nake ina ta juye - juye da zummar barci barawo yaxo yayi awon gaba dani, amma ga abu mafi ban haushi barcin ma baisan inayiba, duk wata tsohuwar hikima ko dabara danasani wadda takawo barci da gaggawa nayita amma ba labari. Ni kadai ne kwal adakin na zubawa rufin dakin idanu, kai kace wani abin nake kokarin tunanowa wanda yadade da shudewa, bakajin sautin komai adakin sai na Radion dake ta babatu ita kadai, da farkon nayi yunkurin kashe radion amma daga baya sai nakoma na kunnata sbd ganin barcin yaki xuwa kuma zaman kadaicin zaimin yawa. Akalla yanzu karfe kusan 12 na dare da wasu yan mintoci amma har kawo yanzu banji alamun wani abuba waishi BARCI atare daniba. Banyi auneba sai naji radion ta tsagaita da surutan dake fita daga gareta, sakamakon hakan sai wani sauti mara dadin ji ketashi Shuuuuu!!! Cikin sauri nakai hannuna kan radion kana na lalubi makashin radion domin tuni nagane cewa gidan radion ne suma suka tattara nasu yanasu domin zuwa su kwanta, wanda kawo yanzun ni ba alamun hakan zaisamu agareni. Abin kamar almara domin har nakai akalla karfe dayan dare idona tarwai ba alamun karuwa nadaga birbishin Gyangyadi balle akai ga xancen Barci. Dole natashi zaune kana na matso da radion kusan dani duk da nasan cewa ba wata tasha da zansamu abude, amma hakan baisa nafasa aniyata ba ta kunna radion, sautin nan dai mara dadin jii shine yakuma biyo bayan kunnawar tawa. Bayan nagama zagaye daga farko zuwa karshe na manunin dake nuna inda ake kamo tashar na radion batare da samun nasarar samun wata tasha akunneba. Nakai hannuna natura wani makunni xuwa gaba, wanda xai sadani da bangarorin tashoshin waje, wato inda ake kamo tashoshin kasashen waje. Anan bangaren kam nasamu tashoshi ba adadi amma duk bana fahimtar abinda suke fada wanda hakan yabiyo bayan banbancin harshe dake tsakanina da mutanen kasashen, a hankali nacigaba da murza turner din radion wato inda tanan ne nake murzawa domin zuwa ga tasha ta gaba. Kamar a mafarki kuma kuma kamar almara, sai najiyo wata murya siririya kamar tana tasowa ahankali daga cikin radion kuma abin mamaki da harshen HAUSA nakejiyo birbishin sautin muryar, kuma abin mamaki muryar maca ce. Cikin nutsuwa nadan kara dawo da hannuna baya domin dai na saita dai - dai kan tashar danakejin ana magana da HAUSA da wannan tsohon daren. Mtswww! Nadoka wani uban tsaki bayan dana tabbatar da cewa narasa tasharma gabadaya sakamakon kokari danake naganin na saita tashar domin jin maganar tarwai! Akalla nakai mintoci 15 inata fama da radio ahannu da kuma LALUBE cikin duhu da xummar ganin nasake dacewa da wannan tashar danaji mai dauke da muryar MACE kuma bahaushiya! Anya kuwa ba kunnuwana bane suka jiyomin gaibu ba? Wacce tasha ce wadda take watsa shirye - shiyenta da harshen hausa kuma wadda take Waje take gudanar da aikace - aikacenta cikin Dare haka? wadannan sune tambayoyin da kwakwalwata take son sanin amsarsu daga gareni. Cak! Nadauke hannuna bayan danaji kamar na kuma dacewa da samo wannan tashar... Na ajiye radion ahankali domin nasamu nadan kwanta kana nakuma saurari me wannan tashar take watsawa ahalin yanzu wanda akalla yanxu kusan karfe daya da rabi. ...haba my Rumy kiyi hakuri mana, kema kanki kinsan cewa bazanso hakan ba ai, kinsan cewa bamu taba haduwa ba face to face, to kuma sai gashi zakiyi Birthday dinki kinga ai yakamata ace dole na na halarci taron ai, kuma kinsan cewa ba karamin abubane xai hanani halartaba, nafadamiki bana kasar ne gabadaya na raka daddy na ne zuwa India zai siyo wasu kaya, to nima bandauka zamu dade haka ba, amma kiyi hakuri my RUMY zan kasance tamkar ina tare dake ne aranar taron bikin Birthday din.... kaima kasan dole nadamu ai my love, kasanfa cewa bani da wani farin ciki sama da kai, kuma naci buri da cewa zaka halarci taron bikin, kasan me kuma... Har daddy na nasa yasiyomana Matoci guda biyu iri daya ni dai duk acikin tarin gifts da daddy na yamin kenan na murnar birthday dina, kuma nace bazan fara hawa motar ba sai kazo kazabi daya sannan nahau tawan, to kuma gashi kace dakyar zaka halarci taron bayan kasan cewa zuciyata cike take da kishirwar son ganinka oh! Am so sorry my Rumy, kiyi hakuri kuma ki kwantar da hankalinki Inshaallahu kafin ranar Birthday dinma mundawo daga indian, ko a ranar muka dawo to daga saukarmu xan tawo gareki, dan haka yanzu inaso ki kuma fadamin full address dinki, kinsan wanda kika turamin ta FACEBOOK andade kuma rubutun yayi kasa dayawa zaiyi wahalar ganuwa yanzu wow! To Allah yasa kudawo kafin ranar ma my love, address dina kuma shine idan kazo RIJIYAR ZAKI kace layin C.R.B gida mai lamba 77 ko kace gidan Alh Nasir C.R.B Kawai, kana zuwa kawai kayimin waya ko ka fadawa mai gadi kace SWEETY dinane yazo kawai... Kasan bantaba ganinkaba shiyasa nake da burin mukasance da juna To shikenan my RUMY duk yadda tayiyu kawai, kuma inafatan mudawo kafin ranar ma, lahadi ne ai ranar ko? eh lahadi my husby to karki damu, bari nabarki ki kwanta nasan yanxu anan nigeria dare yayi sosai... Tuni namike daga kwanciyar danayi sbd sauraron hirar danakeji daga wannan tashar da bansan sunantaba balle mitar ta, banyi auneba sai najiyo wani sauti wanda ke nuna cewa angama amfani da waya wajen yin magana wato duuu - duuu! Kai! Shin me hakan yake nufi ne wai? Ana nufin wai dama idan dare ya tsala tashoshin radio suka kulle sai radion taringa sakalo muryoyin wadanda sukeyin waya kenan? Kodai danshi saurayin yana INDIA ne? kamar yadda naji yace, To waima duk wannan abubuwan dana saurara da gaske ne ma to wai? Wadannan sune tulin tarin tambayoyin dake kaiwa da kawowa acikin raina, can sai naji radion takoma sautin nan mara dadin jii wato Shuuu! Wanda hakan ke ankarar dani cewa ba wata tasha akanta kenan. ...Rijiyar Zaki... Layin C.R.B... Gidan Alh Nasir C.R.B... Idan kazo ka kirani kawai ko kacewa mai gadi SWEETY nane yazo... wadannan kalaman da suka fito daga bakin wadda saurayin yake kira da RUMY sune suka sakani cikin tararrabi da kuma wani bahagon tunani daya ziyarci kwakwalwata anan take. ...daddy na yasiyomin motoci guda biyu ni da kai... Sonake sai kazo kazabi taka sannan nafara hawa tawa, to gashi kace dakyar zaka halarci taron bayan kasan cewa zuciyata cike take da kishirwar son ganinka... kai! Tabdijan! Kaji ya yan masu manyan ALJIHU! Shima wannan kalamin tuni kwakwalwata tagama tariyominshi! Hakika nasan unguwar Rijiyar Zaki kuma nasan cewa unguwar masu manyan ALJIHU ce, to amma kuma bansan layinba balle gidansu budurwar mai sunan turawa RUMY. Tuni kwakwalwata tagama tunxurani da kuma bani shawara akan nagwada wannan saar danake ganin cewa kamar abune mafi sauki. Tuni xuciyata tagama yarda da wannan shawara ta kwakwalwata wadda take bani shawara akan naje ga wannan matashiya mai sunan turawa amatsayin nine SWEETY dinta, tunda ainihin sweetyn baya nigeria ahalin yanzu! kai SAKTAN MOHD baka tunanin kaje kuma katarar ainihin sweetyn nata shima yadawo? Baka tunanin tasan kamannin sweetyn nata a hoto kuwa? Shin kana da number dinta ma tukun? Menene ainihin sunan sweetyn nata? Sannan itama kanta RUMY din menene ainihin sunanta? wadannan sune tarin tambayoyin da wata xuciyata ta lallabo take tuhumata akan dole sai nasamo amsarsu nan take, ni kaina sai yanzu nagane cewa ashe ganin KITSE nakeyiwa ROGO kenan. kada katsaya SHIRIRITA kana biyewa faduwar gaba wanda faduwar gaba asarar namiji ne, maza ka tsaya sanya kaje kayi asarar sabuwar MOTA dal! Kawai kagwada saarka kagani domin ance arashin tayi akan bar araha... Tuni na amince da wannan shawarar wadda wata xuciyar daban ta sadado taxo ta fesamin, dan haka tuni nacika da doki naganin ranar LAHADI tazo domin na xiyarci unguwar RIJIYAR ZAKI domin nagwada saa ta tacin sabuwar MOTA dal Ranar lahadi tun da sassafe nafara tunane - tunane kala - kala gami da shawarwari akan wacca irin shiga yakamata nayiwa masoyiyata ta gaibu wato RUMY, Farin jeans gami da bakar T. shirt sune nazabo ajerin kayana kana na xabi wani bakin takalmi sau ciki da kuma bakin glass duk dai dan ganin na burge budurwa mai sunan turawa wato RUMY! Karfe biyu da mintoci 49 na yammacin ranar LAHADIN nafito daga bakin layinmu da xummar xuwa unguwar RIJIYAR ZAKI....! #ADMIN. SAKTAN MOHD. 08090948640, 07045358573, BBm, pin. 2611A722. Email. SAKTAN MOHD
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:28:33 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015